Na Ƙagu In Tafi Na Bar Fadar Shugaban Kasa-- Muhammadu Buhari 

Na Ƙagu In Tafi Na Bar Fadar Shugaban Kasa-- Muhammadu Buhari 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatarsa ta barin mulki, Daily Trust ta rahoto. 

A lokuta da dama a baya, Buhari ya sha fadin cewa 29 ga watan Mayu kawai ya ke jira ya mika mulki. 
Da ya ke jawabi a taron bankwana da jakadiyar Amurka mai barin gado, Mary Beth Leonard, a fadar shugaban kasa a Abuja ranar Talata, shugaban Najeriya ya ce, ''na kagu in tafi''. 
Ya fadi haka lokacin da ya ke amsa tambaya daga Leonard. 
Ya kara da cewa ya shirya zama ''babban manomi'' da zai dinga aiki a gonakinsa ya na kula da dabbobinsa sama da 300 a Daura, mahaifarsa a Jihar Katsina. 
Buhari, wanda ya bayyana gamsuwa da yadda yan Najeriya su ka nuna muhimmancin dimukradiyya ta hanyar zabar wanda ran su ya ke so a zabukan da aka kammala, ya ce lallai an samu cigaba ta wannan fannin a Najeriya. 
 
''Mutane sun fara gane karfin su. Bayar da damar zaben adalci da gaskiya, ba wanda zai gaya mu su abin da za su yi. Ban ji dadin rashin nasarar wasu daga cikin 'yan takarar ba. 
Amma naji dadi da yadda mutane su ka yi zabinsu, su ka zabi wanda ya ci da kayar da wanda ya fadi.''