Kebbi a shekara 32: Abin Da Aka So Gani Ba Shi Aka Gani Ba

Mi ke hana Burnin Kebbi bunkasa amma ga Argungu da Yauri da Jega sun zama tamkar babban birnin jiha a tsarin gari da jama'a, ya ce "kamata ya yi gwamnatocin da aka yi su ba da muhimmanci wurin raya birni don fuska ce ga masu son saka jari a Kebbi ana daukar in Gwamna ya yi aiki a birni kamar jiha ya yi aiki ba shi ne ya sa suke bunkasa wadan can, lamarin siyasa in gwamnati ta zo ba tsari tau za a same ta da wañnan koma bayan don ana tsoro saboda Gwamna sai ya hau yake tunanin abin da zai yi."

Kebbi a shekara 32: Abin Da Aka So Gani Ba Shi Aka Gani Ba

 

 

 Jihar Kebbi a yanzu ta yi shekara 32 da samar da ita a matsaayin jiha da ke da cikakken iko da ta yi Gwamnoni da dama na soja da farar hula, wasu mutanen jihar na kallon ba wani cigaban a zo a gani da Kebbin ta samu yayin da wasu ke ganin Kebbin ta samu cigaban da ake iya sanar da kowa cikin babbar murya.

Managarciya  ta duba lamarin cigaban in da mutane suka yi bayani kan abin da suka fahimta a tsarin cigaban jihar ta Kebbi.

Kan maganar ci gaba a 'yancin kan jihar Kebbi Honarabul  Abubakar Bagudu Dallatun Kalgo ya ce  "tarihin jihar Kebbi na shekara 32 a wasu fannoni an samu cigaba wasun kuma bata  canja zane ba, ka ga dai in an ce an yi jiha za a yi kananan hukumomi kenan  mulki ya zo kusa ga talakawa, an samar da Kebbi a 1991 lokacin Sakkwato nada yawan kananan hukumomi 19, a ciki aka baiwa Kebbi bakwai, akwai Argungu da Bunza da Bagudo da Yawuri da Zuru da Jega da  Kuma Gwandu da su ne suka samar da jihar sai  aka Kara yawansu suka kai 21 don samar da amfani ga jama'a, yawan makarantu ya karu ilmi ya kusa ga talakawa, an samu yawan asibitoci da karin ma'aikatan gwamnati, tattalin arziki ya karu don jiha na samun kasonta daga gwamnatin tarayya, tau amma in ka lura a gefen sha'ani na shugabanci an tsaya cak ba a yi gaba ba, Kuma ba a koma baya ba, tun sanda aka samu Kebbi an yi shugabanni na soja da farar hula in ka kwatanta jihohi da aka samar tare da Kebbi kamar Abia da Kogi da Jigawa da Delta da Yobe zaka ga fannonin rayuwa sun wuce Kebbi,  ban da jihar Taraba, za ka ga   jihar ba baki masu saka jari duk da Muna da kasar noma da zaman lafiya.

"Wani cikas Kuma shugabanni ba su daurawa Kan aikin Wanda suka gaba ce su a misali tsohon Gwamna Adamu Aleru ya kawo wani tsarin noma mai suna "Ka Tashi" tsari ne mai kyau tun bayan wucewarsa ba sake maganar shirin ba, haka tsohon Gwamna Dakin Gari bai kammala wasu aiyukka ba musamman na sakatariya da asibitin dabbobi haka aka kyale ta, abin da ke nunawa kamar Gwamonin sukan samu Mulki ne ba wani daftari mai kunshe da aiyukkan ci gaba a tare da su, shi ne ya sa aka kasa samun takamammen cigaba, bayan Kuma gwamnatocin ba sa tafiya da ra'ayin jama'a, abin da suka ga dama kawai suke yi, da Kebbi ta samu shugabanci Mai yi don jama'a, da cigaban da za a samu zai wuce misali sai ga shi har yanzu jihar tana rarrafe ba ta tashi da kafarta ba, cigaba da akasinsa suna tafiya kunnen Doki ne kashi 52 cigaba, 48 rashinsa," a cewar Tafida.

Mi ke hana Burnin Kebbi bunkasa amma ga Argungu da Yauri da Jega sun zama tamkar babban birnin jiha a tsarin gari da jama'a, ya ce "kamata ya yi gwamnatocin da aka yi su ba da muhimmanci wurin raya birni don fuska ce ga masu son saka jari a Kebbi ana daukar in Gwamna ya yi aiki a birni kamar jiha ya yi aiki ba shi ne ya sa suke bunkasa wadan can, lamarin siyasa in gwamnati ta zo ba tsari tau za a same ta da wañnan koma bayan don ana tsoro saboda Gwamna sai ya hau yake tunanin abin da zai yi."

Alhaji Yakubu Ahmad BK Kwamishinan yada labarai a jihar Kebbi a mahangarsa an samu cigaba a 'yancin jiha da aka samu "ba zai yiwu a shekara 32 a ce ba a samu cigaba ba hakan duk cigaban da aka samu, ba za a ce ba bukatar Kara kaimi kansu, tun sanda aka samar da jihar akwai wasu kalubale irin samar da gine-ginen abubuwan more rayuwa amma dai gwamnatin da ta gabata ta Atiku Bagudu da wannan dake ci sun yi kokari domin Kebbi na fuskantar koma baya a haujin gine-gine sai godiyar Allah gwamnanmu Dakta Nasiru Idris ya soma gudanar da manyan aiyukka in da yake son a kammala sakatariya ta jiha da aka yi shekara 10 ba a kare ba, ya fara manyan hanyoyin cikin gari domin birnin Kebbi a gaskiya akwai wasu kananan hukumomi da suka fi ta ci gaba, an dauko aiyukka don a cimma sauran takwarorinta da aka kafa su tare matsayin jihohi nan gaba kadan za mu cimma burinmu.

"Shugabanci nagari da kishi  ke kawo cigaba in suka yi aiki tukuru a Kebbi an samu akasin haka a shekarun da suka gabata hakan ya sa har mu 'yan asalin jiha ke kukan ba a samu cigaba ba, Amma dai a yau an dauko hanya," a cewarsa.

Kan batun rashin kishin Birnin Kebbi da mutane suke da shi mi gwamnati za ta yi kan lamarin,  ya ce "wannan kalubale ne babba Kuma shi ne ya Sanya cigaban ya karanta shugabanni masu kishi ake bukata sai yanzu aka samu an kafa tubali da zai sa Kebbi ta ci gaba da samun cigaba ko bayan wannan gwamnan ya tafi."

Mansur Muhammad Argungu yana ganin Kebbi ba ta samu cigaba ba kuma hakan nada nasaba da yanda aka samar da babban birnin ta wanda kuskure ne aka yi a lokacin ba nan ne yakamata ya zama birnin jiha ba domin tun lokacin an fi garin yawan jama'a da masu kudi da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati.

Ya ce samar da birni a jiha Wanda yafi cigaba ake baiwa domin bunkasa ake so ga gari, yanzu kowa ya ga abin da aka yi bayan shekara 32 garuruwan da suka bi birnin Kebbi bunkasa sun Kara wuce shi nesa ba kusa ba, ban ganin akwai sanda za a ci gaba a jihar sai dai duk Wanda ya zo ya kara bunkasa garinsu ga abin da yake so ga fahimtarsa.

Abdulkarim Yusuf Ambursa ya ce Kebbi ta samu cigaba in ka duba yanda mutane ke kasuwanci da neman ilmi da yanda gwamnatoci ke kokarin bunkasa ilmi abin da yakamata dai jagorori su yi bai wuce shimfida adalci ba don shi ne komai da komai, domin akwai bukatar samar cigaba da yafi Wanda ake da shi a yanzu musamman a haujin ilmi da noma da kiyon lafiya.

Ya ce Kebbi adalci kawai take bukata wurin shugabanni don komai tana da a gefen jama'a da albarkatun kasa ga Kuma yawan kasa da kabilu, duk sanda aka samu shagabq Mai adalci Kebbi za ta wuce tsara ta cimma na gaba da ita a gefen cigaba.