An ga watan Ramadan a Nijeriya----Sarkin Musulmi

An ga watan Ramadan a Nijeriya----Sarkin Musulmi

Mai martaba Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a yau Laraba abin da ke nufin tashi da Azumin Ramadan a gobe Alhamis.
Sarkin musulmi a fadarsa  bai fadi wuraren da aka ga watan ba sai dai ya ce "yau laraba 29 ga  watan  Sha'aban hijira 1444 daidai da 22 ga watan Maris an kawo karshen watan Sha'aban.
"Mun samu labarin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci wurare da yawa a kasar nan kuma kwamitocin ganin wata sun tantance sahihancin bayanan, bisa ga haka gobe Alhamis 23 ga Maris ta zama daya ga watan Ramadan,"a cewar Sarkin Musulmi.
Ya yi kira ga al'ummar musulmi bayan kammala zaben 2023 da su dage da addu'a domin samun cigaban kasa da jihohi.
Ya kuma nemi masu kudi a cikin al'umma da su taimaki talakkawa da gajiyayyu a lokacin ibadar azumin Ramadana musamman abinci da sauran abubuwan bukata.