Ramadan: Sarkin Musulmi ya umurci musulmai da su duba sabon wata a ranar Laraba

Ramadan: Sarkin Musulmi ya umurci musulmai da su duba sabon wata a ranar Laraba

Sarkin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Zubairu Usman-Ugwu, daraktan gudanarwa na majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya fitar a ranar Litinin.

Ramadan lokaci ne da al’ummar musulmi a duniya suke azumin kwanaki 29 ko 30.

A cewar sanarwar, idan ba a ga wata ba a ranar Laraba, za a fara azumi ne kai tsaye a ranar Alhamis.

“Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Shugabanta kuma Sarkin Musulmi, Mai Martaba Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, yana taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar watan azumin Ramadan na shekarar 1444H. Majalisar tana addu’ar Allah ya gafartawa kowane musulmi, ya shiga cikinsa kuma ya amfanar da ibada mai girma,” in ji sanarwar.