Na Ɓata Goma.....Fita ta Farko

Na Ɓata Goma.....Fita ta Farko
*NA BATA GOMA....!*

*5STARS EXPENSIVE COMPANY*

*RUBUTAWA; MARYAM IBRAHIM (DOCTOR MARYAMAH)*

*Bisimillahir Rahmanir Rahim*

*Shafi na farko.*

'Matsanancin laushin dake ƙara ratsa dukkan sassan jikina shi ne ummul'aba'isan ƙara lafewata, tare da ƙara baje jiki ina jan bargo kan jikina. Shi ma bargon sanyi haɗi da laushi na musamman na ƙara jin ya yi, cike da zallar shauƙi na ke ƙoƙarin miƙa hannuna domin in lalaubo Auta inji wanne sashe ta ke, dama ne ko hagu? Kasancewar ina ɓararrake ne a tsakiyar gadon. Ƙusa ƙusa, laushi laushi, cike da tauri taurin abu su ne suka yiwa hannu na maraba da sauka, cike da azama na buɗe idanuwana, sai dai kaf ɗakin ba zaka samu ganin ko da tafin hannunka ba ne a ciki, saboda tsabar duhun da ya mamaye ɗakin. Miƙa hannuna na yi ƙarƙashin pillow da zummar ɗauko fitila, sai dai wayam! Bata gun da nake ajiyeta. Miƙewa zaune na yi na ƙara miƙa hannu a gefen damana, sai dai me? Cikin abu mai ɗaumin gaske hannuna ya sauka, ga sulɓin abu da ke ƙara lulluɓe hannun nawa da shi. Cike da karsashi na wangale baki da niyar ƙwala ihu ko zan samu mai kawomin ɗauki. Sai dai kash! Ƙame bakina ya ƙame a wangale, wanda hakan ya yi daidai da bayyanar wani haske mai barazanar tarwatsa kwayoyin idanuwana. Rufe idanuwan naje yi, sai dai ina! Hakan bai samu ba, kamar yadda bakina ya ke a wangale haka idanuwana suka kasance buɗe tarrr! Dirar abu na ji a tsakiyar ɗakin, hakan ya sanya ni kai kallona a wurin. "Ya Allah" ita ce kalma ta farko data fara bayyana a gareni a can ƙasan zuciyata. 'ya'yan biri ne birjik a ɗakin suna wasan kokowa wa'yanda a ƙalla za su kai su goma sha! Sai a lokacin na ke jin tashin sautin gurnaninsu, cike da zallar mamaki haɗi da buguwar zuciya na ke binsu da idanuwana wa'yanda ke wangale har izuwa lokacin, ga bakina wangale shima kamar abinda aka sa ƙarfe akayi tangali haka na ke jin shi, domin kuwa na kasa rufe shi. Dire dire Kawai su keyi a tsakiyar ɗakin suna fursas da 'yan ƙananun sauti ƙasa ƙasa. Saurin ɗauke idanuwana na yi kansu na mayar gefen damana domin ganin meya hananin jin Auta? Ko ta shiga banɗakine ba ni da labari? Wata jibgegiyar halitta ce idanuwana suka yi tozali da'ita kwance a gefena, fitar da halshe kawai ta ke yi tana mayarwa, sai kuma ta koma lasan dukkan sassan jikinta. Ruɗani! Shi ne ya mamaye kafatanin ilahirrin ruhina! Meke shirin faruwa ne wai? Na faɗa a ƙasan raina, domin kuwa magana ta gagare ni a baki. Ƙwala ƙwalan idanuwanta dake jazur da su ta wangale, haɗi da ƙara wangale idanuwanta a kaina, lokaci ɗaya muka saki kuwa mai rikita ƙwaƙwalwa a tare! A lokacin ne numfashina ya samu nasarar yin fitar burgu daga gangar jikina na 'yan wa'yansu mintuna!
                          ★★★★★
Jijjiga jikina da a keyi ne da gunjin kuka sama sama, su ne suka fara ziyartata. Kara runtse idanuwana na yi gudun kar in buɗe inyi tozali da abinda yafi ƙarfina. "Habiba, Habiba ke, maza buɗe idanuwanki"  Jin Muryar Babanmu da na yi kusa da kunnena ne ya ɗan ragemin fargaba, amma duk da haka ban buɗe idanuwan ba. "Ki buɗe idon a kace mana" ya ƙara faɗa cikin faɗa faɗa, kasancewarsa mutum mai tsauri tsauri. Sanin halinsa ne ya sanya ni shahadar buɗe idanuwana. Shi da Maah nayi kiciɓis da su a gabana, gefe can ɗan nesa da ni Auta ce zaune a ƙasa tana gunjin kuka.  "Alhamdulillah" cewar Maah tana taɓa jikina, "Habiba meke damunki? Allah yasa ba abinda ya same ki 'yata" kallon sama da ƙasa Babanmu ya watsa mata, kamin cikin ya mutse fuska ya miƙe tare da kakkaɓe jikin shi, ya faɗa ɗakin Mama Hauwah. Daga ni har Maah da Auta da ke kuka da kallo muka bi shi, ko waccenmu da abinda ke ranta.
Sauke idon da zanyi kan Maah, ba sai naga ta komamin irin waccen halittar da na yi tozali da ita ba a dare! Cikin kiɗimewa da ruɗewa na buga wata irin razananniyar kuwa mai barazanar tarwatsa kunnen mai saurare!
Daga Babanmu har Mama Hauwah rige rigen fitowa daga ɗakin su ke yi hannu bisa kai, sai gwalalar idanuwa su ke yi. "Meya faru?" Cewar Babanmu yana buɗemin ido. Juyowa na yi na sake ganin yadda halittar Maah ke ƙara rikiɗewa tana komawa komawa sak waccan halittar. "Allah" na faɗa cike da firgici ina me jan jikina daga wurin da na ke da zummar in samu in miƙe zaune. Miƙa hannu ta yi da niyar kamo nawa na tsandara ihun neman agaji ina me cewa "Baba, kace karta taɓa ni, ka ɗauke ni daga nan, canye ni za tayi" Kallon kallon su ka yi shi da Mama Hauwah, kamin shi ya buɗe baki cikin rawar murya ya ce".....!

*Allah ya gafartawa iyayenmu. Amin.