Minista ta raba wa mata POS guda dubu 37 tare da yi musu gargaɗi mai zafi

Minista ta raba wa mata POS guda dubu 37 tare da yi musu gargaɗi mai zafi

Uju Kennedy-Ohanenye, ministar harkokin mata, ta gargadi mata da kada su siyar da ko kuma sauya injunan cirar kudi, POS, dubu 37,000 na kyauta a fadin kasar.

Kennedy-Ohanenye ta yi wannan gargadin ne a jiya Alhamis a Abuja a lokacin kashi na farko na rabon POS guda 1,000 kyauta ga wasu mata a babban birnin tarayya Abuja.

Ministar ta ce shirin da hadin gwiwa da PLUG Platform Group ne, kungiyar da ke rajin kowa ya samu bunkasar tattalin arziki.

A cewarta, POS zai tabbatar da samun saukin kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arzikin mata a Najeriya.

"Idan kun san cewa ba za ku yi amfani da wannan POS da kanku ba to kar ku karɓa.

“Wasunku suna tunanin cewa wani abu ne da za su sayar, to kuwa dan kun sayar, za ku ji ba dadi.

“Kafin a ba ku wannan POS, tabbas an yi muku rajista a cikin tsarin kuma za mu ci gaba da bin diddigin ku. Idanuwanmu suna kanku," in ji ta.