Bello Turji Ya Zargi Matawalle da Goyon Bayan Ta’addanci

Bello Turji Ya Zargi Matawalle da Goyon Bayan Ta’addanci


Gawurtacen dan bindiga, Bello Turji ya zargi Ministan tsaro, Bello Matawalle da daukar nauyin ta'addanci. 

Bello Turji musamman ya kira suna tsohon gwamnan Zamfara da cewa shi ya daurewa ta'addanci gindi wanda ya ki karewa.

 
Dan ta'addan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa wanda @Miniko_jnr ya wallafa a shafin X. 
Turji ya ce yana da hujjoji da zai kare zargin da ya yi na cewa gwamnatin da ta shude ita ta daurewa ta'addanci gindi a jihar. 
Ya ce mutane da dama dake Bauchi ko Kaduna ba za su iya sanin abin da ke faruwa na matsaloli a jihar Zamfara ba. 
"Gwamnati tana daurewa ta'addanci gindi, akwai wasu mutane daga Zurmi da Shinkafi da Issah ba za su musanta wannan bidiyo ba." 
"Ina mai tabbatarwa Gwamnatin Tarayya idan ba su sani ba, zan kira sunaye da hujjoji, ina bukatar da su binciki ayyukan wadannan mutane, na rantse da Allah gaskiya nake fada." 
"Gwamnatin Zamfara da ta shude karkashin mulkin Bello Matawalle ta tatauna da 'yan bindiga amma kuma ita ta kawo cikas kan lamarin." 
Bello Turji ya kamata gwamnati ta fito ta fadi gaskiya kan abin da yake faruwa domin ta bar zargin wasu kan wannan matsalar.