Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan Majalisar Dunkin Duniya 

Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan Majalisar Dunkin Duniya 

 

Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya sun yi taro tare da tawagar Majalisar Xinkin Duniya, qarqashin jagorancin mai kula da harkokin jin qai, Mohamed Malick Fall, a Abuja ranar Juma'a.

 

Manufar taron dai ita ce neman tallafi don tunkarar babban qalubalen ci gaban yankin.

 

Taron wanda Shugaban Qungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranta, ya samu halartar gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Kano, Mallam Umar Namadi na Jigawa; Mataimakin Gwamnan Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal.

 

Taron wanda aka gudanar a zauren Majalisar Xinkin Duniya da ke Abuja, ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi matsalolin tsaro, da talauci, da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Gwamnonin sun kuma bayyana damuwarsu game da qaruwar shan miyagun qwayoyi, yawan mace-macen yara da mata masu juna biyu, da rashin aikin yi ga matasa. 

Sun qara bayyana tasirin qalubale kamar gurvacewar qasa da sauyin yanayi kan noma, wanda kusan kashi 80 na al'ummar qasar ke dogaro da su.

Bugu da qari, gwamnonin sun jaddada illar matsalar qarancin abinci mai gina jiki ga qananan yara. 

Shugaban Qungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, ya jaddada buqatar samar da tsarin haxin kan yankin, inda ya ce, “Hanya xaya da za mu iya shawo kan qalubalen Arewa maso Yamma ita ce hanyar da ake bi a yankin da ke buqatar mu haxa kai ta hanyar haxin gwiwa. Ya kamata mu haxa karfi da qarfe wajen yaqi da talauci da rashin aikin yi, kasancewar manyan su abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a yankin.” 

Sai dai kuma Babban Jami'in Kula da Ayyukan Jin Qai na Majalisar Xinkin Duniya Mohamed Malick Fall, ya nuna farin cikinsa ga taron tare da tabbatar da aniyar Majalisar Xinkin Duniya na tallafa wa yankin na Arewa maso Yamma. 

Ya bayyana muhimmancin rawar da yankin ke takawa wajen cimma muradun ci gaba mai xorewa (SDGs) a Nijeriya, wanda hakan zai amfani xaukacin nahiyar Afirka. 

“Majalisar Xinkin Duniya a Nijeriya tana da qwarin gwiwar ganin qwaqqwaran jagoranci da jajircewar Gwamnonin Arewa maso Yamma na inganta rayuwar al’ummarsu. Za mu ci gaba da tallafa wa gwamnati da al’ummar Arewa maso Yammacin Nijeriya. Tare, za mu ceto da kuma hanzarta ajandar 2030 don ci gaba mai xorewa a yankin, "in ji Fall.

Fall ya qara sanar da gwamnonin game da yadda Majalisar Xinkin Duniya ta mayar da hankali wajen hanzarta cimma nasarar SDG ta fannoni shida: tsarin abinci, ilimi, kariyar zamantakewa da ayyukan yi, samar da makamashi, sauyin yanayi, da sauyi na dijital.

An kammala taron ne da yarjejeniyar samar da taswirar aiki, da tawagogin fasaha daga Majalisar Xnkin Duniya da na jihohi bakwai za su tsara, bisa tsarin tallafin Majalisar Xinkin Duniya ga yankin.