Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, biyo bayan bayanin da jami’an tsaro suka yi masa ya bayar da umurnin a sassauta dokar hana fita da aka sanya a birnin Sakkwato.
Bisa ga wannan umurnin, yanzu an hana fitar ne daga faɗuwar rana zuwa wayewar gari a birnin Sakkwato da kewaye.
Kuma an yi hakan ne domin a baiwa mutane dama su fita neman abinci da sauran sana’o’in su.
A sanarwar da Kwamishinan Yada labarai Isah Bajini Galadanchi ya fitar a ranar litinin ya ce saboda haka gwamnati na bada shawara a gare mu da mu tabbatar da zaman lumana a tsakanin mu, domin ba za a lamunce ma duk wani nau’in taka doka da oda ba a wannan jaha.





