MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 17
Page 17
Tana shiga ɗakin cikin masifar ta aje kaskon hayaƙinta ta fara cuku-cukun cire kayan fulanin da ta saka ne idanta ya kai kan madubin ɗakin, ido ta sake warowa waje tana kallon madubin dan ƙara gasgata abin da ta ke hange cikinsa. "Na shiga uku ni Huraira ubanme ya kawo tsagar ƴan bori ga fuskata haka? Ida isa gaban madubin tayi ai kuwa taga wata mahaukaciyar tsaga caba-caba ga fuskarta ba kyan gani duk jini ya bushe, "Malam kana ina kazo kaga abin mamaki ni Huraira na shiga tara na fice ashirin" ko motsi bai ba duk da yaji yanda ta ke ihun yaje ya gani, yau kam ta kaishi inda bai tsammanin zasu daidaita saboda ba zai lamunci shirka a cikin gidansa ba, Bilkisu ce ta nufi ɗakin da saurinta, Mal Ahmad ya dakatar da ita cike da takaici ya dubi Bilkisun yace "Ɗiyar kirki kar kije rabu da ita dani ta ke magana" ba dan ta so ba ta koma ɗakinsu tana hawaye har ga Allah tana jin tausan Innar tasu domin tana hanyar da ba ta bullewa ko kaɗan.
Inna kuwa kamar wasa ta ga fuskarta na sauya wa zuwa ta wata Bafulatana dake kawo masu tallar nono sak, ji tayi an kamo hannunta, cike da tunanin malam ɗinne yasata fisgewa da cewar "Malam ai nasan ba ƙaunata kake ba yanzu, dan haka baka damu da duk uwar data dameni ba, to kaima kanka danni da ka soni da karka soni uwarsu ɗaya ubansu ɗaya"sai da ta kai aya sannan ta kalli bayanta inda aka rike mata hannun. "Ihu kuzo aljanna Malam! Na shigesu Malam Bafulatanar Aljana kaina. "A aradun Allah bama son wauta ni zaka tarama bil'adama a bayan kai ka kirani? Zuwa lokacin babu inda bai rawa jikin Huraira tsabar firgita da tsoro, cikin kallon ƙulurra Bafulatanar tace "A kana kiramu kana zaginmu a zaka ci ubanka aradun Allah yau" Inna Huraira baki ya datse tunanin addu'ar koran fulanin aljannu da kakarta ta koya mata tun tana ƙarama ta ke yi,amma ta kasa tuno ko da kalma guda ce daga cikin addu'ar, mari ta ko ina Aljanar ta dinga zabga mata hakan yasa ta cika gidan da ihu. Dole Malam ya nufo ɗakin Hurairar dan yaji abin ya zarce tunaninsa, yana shiga yaganta sai wata birgima ƙasa ta ke tana ihu ta rufe fuskarta. "Ke yanzu Huraira har abin naki ya kaiga hawa bori? Jin muryar Malam yasata ƙara ƙarfin ihunta wai ita nan dan ya tausaya mata, sai abin ya ƙume Malam ɗin ya fice ɗakin,sai gashi da uban rushi ya aje yace bari dai na taimaka maki naga lamarin naki azimun ne, ya kawo uban barkono (yaji) ya zuba cikin rushin yayi wuf ya fice daga ɗakin ya ja mata ƙofar ya rufe.
Kullum sai Yah Malam yaje gun Nasir sun zanta sosai wata shaƙuwa ta shiga tsakaninsu, shi dai Nasir duk tunaninsa Yah Malam ɗan uwansu Bilkisu ne kuma gidansu yake zaune, sai dai akwai abubuwa da dama da yake son tambayar Yah Malam ɗin amma ya kasa, ko da yaushe tare suke zuwa gun Bilkisun su yi ta fira kowa nasan tambayar kowa ina labarin yah Malam ɗin Bilkisu da Nasir amma sai su kasa tambayar, gaba ɗaya kowa yasan Bilkisu da Nasir soyayya suke a layin nasu, wanda jira ake kawai Bilkisun ta shiga aji shida a saka ranar auren nasu.
Malam Aminu kwance ɗakin mamarsu ana jinyarsa amma bai iya ko daga halshensa balle yayi magana, jikinta duk ya kwaye kamar wanda akaima fallatsin ruwan zafi tafasasshe, sai da ya kwana ya wuni sannan ya farfaɗo daman gashi magana ta gagara daga garesa,da ya rufe idonsa ganin Bilkisu ya ke tana cin naman kan mutum. A kwana na biyu ne ya tashi garau hatta tuyar dake jikinsa babu ita ta ɓace,abin da yaba mutanen gidansu mamaki kenan, ya shirya tsab ya tafi makaranta domin yasan cewa acan ne kawai yafi karfin sihirin Bilkisu, acan ne kawai zai iya ɗaukar mataki kanta bata da yanda zata yi dashi, dan haka yayi alƙawarin yau idan taje sai yayi mata abin da aljanu ma basu iya ɗauka.
To fa komi yake nufi ?
Ko ya Inna zata yi da maganin da malam yasa mata ?
Ku dai sake jiran Haupha dan jin cigaban labarin.