Matsin Rayuwa: Ƙungiya ta Ƙaddamar da Rabon Abinci da Littafai ga Marayu da 'Yan Gudun Hijira a Sokoto 

Matsin Rayuwa: Ƙungiya ta Ƙaddamar da Rabon Abinci da Littafai ga Marayu da 'Yan Gudun Hijira a Sokoto 

Kuncin Rayuwa, a  Sakkwato,Wata Kungiya ta kaddamar da Rabon  kayan Abinchi da   karatu da rubutu ga Marayu,Yan Gudun Hijira, da ɗalibbai maras Hali..

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.      

Wata kungiyar .ƴan Ƙasa masu kishin Cigaba ta "Concerned Citizens of Likes Minds (CCLM)" ta kaddamar da Rabon tallafin kayan Abinchi da kayan karatu da rubutu ga Marayu da ɗalibbai, 'yan Gudun Hijira da sauran mabukata,a jahar Sokoto.
Ita dai kungiyar "Concerned Citizens Of Likes Minds (CCLM)" kungiya che wadda aka Assasa wadda ke da Wakilchi ako ina cikin faɗin Nigeria daga  Harda Sokoto.
Kungiya che da aka zo da itah domin tallafawa Al'umma musamman marayu da masu karamin karfii da ɗalibbai, domin ganin an inganta Rayuwar su kamar kowa a ko ina cikin faɗin Kasar nan daga chiki Harda Sokoto.
Wannan ne yasa kungiyar tayi tattaki ta garzayo Sokoto inda aka kaddamar da kayan Abinchi a gidan marayu, da kayan Abinchi ga ƴan gudun hijira, tare da kaddamar da littafan karatu da rubutu ga wasu makarantu na jahar Sokoto, karkashin jagoranchin shugabar kungiyar Chairlady Hajiya Madina...
Wannan dai anyi shine duka cikin  namijin kokarin shugaban ma'aikatan Tsaro na kasa (Chief Of Defence Staff) Christopher Musa ga jahar Sokoto domin saukakawa rayuwa musamman a wannan Lokachi da ake fama da tsananin rayuwa da rashin tsaro.
Sakataren kungiyar na ƙasa, Comrd Ibrahim Riskuwa  yayi kira ga wayan da suka amfana da suyi amfani da abinda suka samu ta hanya mai kyaw, tare da jan hankalin ɗalibbai da su mayarda hankali ga karatu wurin zama jekadu na gari abin alfahari ga Sokoto da Nigeria baki ɗaya