Mahara sun kashe mutum 6 a wani sabon hari a Sokoto

Mahara sun kai wani farmaki a ƙauyen karamar hukumar Tangaza dake Sakkwato sun kashe mutum shidda ciki har da matan aure biyu.

Manema labarai sun samu bayanin maharan sun yi wa ƙauyen Saminaka wanda mafiyawansu mafarauta ne da safiyar Lahadi.
An kawo hari ne a lokacin da mafi yawan mutanen sun tafi farauta.
Har yanzu dai ba a gane ko harin da aka kawo na ramuwar gayya ne kan 'yan bindiga 13 da aka ƙone da wuta a Tangaza a ranar Assabar.
Sun harbe matan aure biyu suka yi wa matasa huɗu yankan rago.
Dukan 'yan sa kai dake garin sun shiga daji domin ganin ko za su samu nasarar kama 'yan bindigar. A cewar wata majiya.