Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Datse Babban Titin Kano Zuwa Maiduguri
Ambaliyar da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama ya yanke babban titin Kano zuwa Maiduguri a dai dai tsakanin ƙauyukan Malori da Guskuri a yankin ƙaramar hukumar Katagum da ke jihar Bauchi.
Ambaliyar ta datse tare da raba titin, da kuma haifar da ƙaton rami a tsakani, lamarin da ta tilasta wa matafiya sauya hanya.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye kan titin, tare da kiran mafiya su sauya hanya.
Yayin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo wa titin ɗauki.
Gwamnan ya kuma bayyana muhimmancin titin wanda ke ɗaya daga cikin muhimman titunan da suka haɗa arewa maso gabashin ƙasar da sauran yankunan arewacin ƙasar.
Jihar Bauchi na ɗaya daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ke fuskantar ambaliya a wannan shekara, lamarin da ya haifar da ɓarna mai yawa a wasu ƙananan hukumomin jihar.
managarciya