Ma'aikatar tara haraji a Zamfara ta samo hanyoyin tattara harajin don cigaban jihar

Ma'aikatar tara haraji a Zamfara ta samo hanyoyin tattara harajin don cigaban jihar
Ma'aikatar tara haraji a Zamfara ta samo hanyoyin tattara harajin don cigaban jihar.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
 Ma'aikatar tattara haraji ta jihar Zamfara tace ta samar da wasu hanyoyin tara haraji domin kara tattalin arziki da ci gaban jihar, har da kasa baki daya.
Wannan bayani ya fito daga bakin daraktan mulki na ma'aikatar Alhaji  Muhammad Lawal Mukhtar, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara. 
Yace tuni gwamna Bello Mataalle ya kaddamar da dokar yanda za'a samu hanyar tattara haraji a cikin ma'aikatar domin kaucewa almun dahana da kudaden da aka tara.
Muhammad lawal ya kara da cewa tuni har an kara kudaden harajin da ake karba gun jama'a bayan sun duba yanda ake aikin karbar harajin a lokacin baya, inda suka ga ya kamata a dan kara kudaden domin samun yiwa al'umma ayukkan  ci gaba a fadin jihar.
Da yake tsokaci kan zanga zangar da yan acaba  sukayi, daraktan sai yace wannan abun da ya faru rashin fahimta ne kawai tsakanin su da shuwagabannin su, amma bada ma'aikatar ba.
 Muhammad Lawal ya kara da cewa, ma'aikatar tana nan tana aiki tukuru domin ta mayar da hanyar karbar harajin  yan acabar  ta zamani, domin kaucewa matsalolin yau da kullum, kuma a fitar da jihar daga kangin talauci.
"Nan bada jimawa ba zamu fara yi masu rajista irin ta zamani, domin musan ko su nawa ne ke aiki, kuma yin hakan zai kara taimaka muna wajen  shawo kan matsalar tsaron da muke fuskanta.
"Ya zama dole gare mu mu kara kudin da ake karba ga yan acabar  daga naira ashirin zuwa naira hamsin, saboda irin matsalar tattalin arziki da kasa ke fama da ita. Bayan haka zamu tabbatar da kowane dan acaba ya biya harajin sa domin a kara samun kudaden da za'a gyara masu hanyoyin da suke bi suna sana'ar su"inji darakta.
Da karshe ya ce membobin na yan acaba sunyi zargin cewa kamar an hada kai ne da shugaban su domin a cutar da su, amma daga baya sun fahimta, kuma suka watse.