Kungiyar Malaman Jami’a Sun Kalubalanci Gwamnatin Sakkwato Kan Saba Doka

Kungiyar Malaman Jami’a Sun Kalubalanci Gwamnatin Sakkwato Kan Saba Doka

Kungiyar malaaman jami’a ta Nijeriya waton ASUU sun kalubalanci gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto kan saba dokar tafiyar da jami’o'i in da ake yi wa doka karan tsaye a  wurin tafiyar da jami'a mallakar jiha.

Farfesa Abubakar Sabo shugaban kungiyar na yankin Sakkwato  ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a satin da ya gabata cikin Sakkwato ya ce ASUU ta fahimci yadda 'yancin gashin kai ke samu cikas a jami'o'in Nijeriya wanda hakn ya kai ga rushe majalisr gudnarwar jami'o'i ba bisa ka'ida ba.

"A yauzu jami'o'i a kasa da jihohi shugabaninsu ne ke gudanar da komai da hadin bakin ma'aikatun ilmi wanda hakan sabawa doka ne.

"Ba su da hurumin bayar da kwangila, karin girma, daukar ma'aikata sai an cika sharudda, ASUU ta yi tir da lamarin da ba  sabon ba."

Farfesa Sabo ya yi kira gwamnatin Sakkwato da tarayya su gyara lamarin tafiyar da jami'a wurin samar da majalisar gudanarwa waton Governing Council  da kuma dawo da wadanda wa'adinsu bai kare ba.

Haka ma ya jawo hankalin shugabanin Jami'a su daiana kai bukatun da majalisa ne za ta zartar da su wurin ma'aikatun gwamnati don neman amincewa yin hakan zai iya kawo cikas ga daurewar jami'a a gaba.