Akwai Bukatar Gwamnatin Sakkwato Ta Kara Hutun Shayarwa Ga Mata Zuwa Wata 6
Mutanen da suka halarci taro kan wayar da kan mata muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa a zalla tsawon wata shidda ba tare da an hada shi da komai ba, sun bukaci gwamnatin Sakkwato ta kara wa mata wa'adi a hutun shayarwa daga wata uku ya koma shidda kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi.
Taron wanda aka gudanar a Otal na Dankani domin tunawa da ranar shayar da nonon uwa, mafiyawan mutane sun aminta da kiran don a samu karin lokacin zai taimakawa mata masu aikin gwamnati su yi shayarwar ba wata tsangwama.
Babbar sakatariya a Ma'aikatan mata da kananan yara ta jihar Sakkwato Hajiya Aisha Dantsoho ta ce suna karawa mata kwarin guiwa don su shayar da jarirai nonon uwa zalla, Shirin da ake son yi na samar da wuri na musamman ga mata zai taimaka kwarai ga samar da abin da ake bukata.
"Rashin in da mata za su shayar na musamman ga ma'aikata yana kawo cikas ga cimma bukatar da ake da ita, haka ma akwai bukatar gwamnati ta kara yawan hutun haihuwa ga mata zai taimaka ga samun wadataccen lokaci ga shayarwa, ma'aikatar mata na kokarin wayar da kai kan harkokin mata a samu tsari zai taimaka sosai," a cewarta.
Farfesa Rabi'u Umar Aliyu ya ce taron na da muhimmanci da amfani a Sakkwato domin shayar da nono uwa zalla zai taimaki uwaye da yara don kariyar cirutoci dake kamuwar yara.
Ya ce a wayar da kan shayar da nonon uwa koyaushe da samar da wuri na musamman ga mata don su shayar da nono a lokacin da suke wurin aiki ba tare da wata tsangwama ba, gwamnati ba ta biyan komai ta samar ne kawai, bayan bukatar da ake da ita na kara yawan lokacin hutu ga uwa mai shayarwa don samar da shayarwa tsintsa, akwai bukatar gwamnatin Sakkwato ta duba kara hutun na mai haihuwa saboda cimma abin da ake bukata.
Hajiya Zainab Ahmad Binji tsohuwar Amira a kungiyar mata ta FOMWAN kuma ma'aikaciyar lafiya ta ce wannan kokarin da ake yi na mata su rika shayar da nono zalla ga yara har tsawon wata shidda abin da zai taimake su ne da lafiyar yara abu ne da yakamata su aminta da shi don zai taimaki kiyon lafiyarsu gaba daya.