'Yan Fansho Sun Gudunar Da Zanga-Zangar Neman Gwamnati Ta Biya Su Hakkinsu Na Garatitu a Jihar Neja

'Yan Fansho Sun Gudunar Da Zanga-Zangar Neman Gwamnati Ta Biya Su Hakkinsu Na Garatitu a Jihar Neja
 

 

From Awwal Umar Kontagora

 

Tsoffin ma'aikata da suka ajiye aiki a jihar Neja waton 'yan fansho sun yi dirar mikiya a gidan gwamnatin jihar domin neman hakkinsu da gwamnati ta kasa biya bayan bayan sun kwashe shekara 30 wasu 35 suna sadaukarwa a jihar, a karshe hakkinsu ya gagara biya. 

'Yan Fanshon sun yanke shawarar yin hakan ne domin sun fahimci shi ne kawai yaren da gwamnati ke fahimta ta san suna nan cikin halin kunci.
Mataimakin gwamna a jihar da yake yi wa 'yan fanshon bayani cewa su yi hakuri a cikin wannan gwamnati ta Lolo zai yi iyakar kokarinsa ya biya dukkan hakkin 'yan fansho a jihar, ya kasance a gefen garatitu basa bin gwamnati bashi.
An zabi mutane 10 a cikin 'yan fanshon da za su zauna tare da mataimakin gwamna a ranar Alhamis.
'Yan Fansho suna cin bakar wuya a jihar Neja, gwamnati ta ce za ta yi kokari ta biya su nan ba da jimawa ba.