Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa EFCC Ta Amince Da Sauya Fasalin Takardun Kudin Najeriya

Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa EFCC Ta Amince Da Sauya Fasalin Takardun Kudin Najeriya

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce tana tare kai da fata da babban Bankin Najeriya CBN a kan sabbin takardun kudin Naira da za a fara aiki da su a tsakiyar watan Disamba mai zuwa.

 
A hirarahi da muryar Amurka Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashin Bawa ya ce yin haka yana da muhimmanci kwarai domin zai taimaka wajen sanin kudaden da ke na kwarai da wadanda ba ba kwarai ba.
 
Bawa ya ce yanzu sun zo a matsayinsu na kasa Najeriya wadanda kudaden da babban bankin ya ce yana da su ke zagayawa a Najeriya kashi 85 cikin 100 na hannun mutane inda kashi 15 cikin 100 ne kawai ke bankunan Najeriya to ta wannan hali ya ya zaka kawo tsarin kudi da zai duba sha'ani na kudade ya zamanto da cewa zai yi tasiri ai ba zai yi tasiri ba.
 
Ya kara da cewa dole ne CBN ta dauko wani mataki wanda za ta fara tun daga kasa da za ta rinka saka ido na wadannan abubuwa wannan abun mun yi na'am da shi zai taimaka mana wajen ayyukanmu zai taimaka mana a abubuwa da yawa nasara ba wai lallai a ganta yanzu ba amma idan Allah ya so nan gaba kadan za'a ganta in ji shi.
 
EFCC ta bukaci yan Najeriya su bata hadin kai a yaki da rashawa.