Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna
A Yammacin yau laraba 04/05/2023 Allah ya dauki rayuwar tsohon shugaban kungiyar tsoffin kananan hukumomi ( ALGON) Hon. Gambo Tanko Kagara.
Kafin rasuwarsa ya shugabanci karamar hukumar Rafi daga 2015-2019, inda bayan samun nasarar darewa bisa kujeran shugabancin kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar Neja, saboda kwazo da jajircewarsa wajen samar da ababen more rayuwa ga al'ummomin karkara, aka zabe shi shugabancin ALGON na tsawon shekaru biyu.
Marigayi Hon. Tanko Kagara, kafin rasuwarsa, shi ne babban mai baiwa gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello shawara akan harkokin kananan hukumomi da masarautu.
Marigayin yayi fama da jinya mai tsawo kafin Allah ya dauki rayuwarsa. Ya rasu ya bar matar aure daya, yaya da jikoki.