Majalisar Dokokin Sakkwato Ta amince Tambuwal Ya Karɓo Bashin Biliyan 28.7

Majalisar Dokokin Sakkwato Ta amince Tambuwal Ya Karɓo Bashin Biliyan 28.7
Tambuwal

Majalisar Dokokin Sakkwato Ta amince Tambuwal Ya Karɓo Bashin Biliyan 28.7

Majalisar dokokin jihar Sakkwato sun amince da gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya karbo bashin biliyan 28.7 ga jihar Sakkwato.
Manema labarai sun dauko bayanin amincewar   ne bayan wasiku guda biyu da gwamnan ya aikawa majalisar kamar yadda jagoran 'yan majalisar APC Bello Isah Ambarura ya karanta buƙatar.
Bukatar ta Tambuwal ta hada da neman gudunmuwar bashi daga gwamanatin tarayya na biliyan 18.7 sai biliyan 10 amadadin dukkan kananan hukumomi 23 na jiha.
Ambarura ya ce neman tallafin wani bangare ne na cikin biliyan 656.1 da shugaba Buhari ya amincewa jihohi 36 na tarayyar Nijeriya.
Mataimakin shugaban majalisa Abubakar Magaji ne ya jagiranci zaman majalisa aka jefa ƙuri'ar amincewa ta hanyar murya in da majalisa ta amince da ciyo bashin kamar yadda aka buƙata.