Ya Kamata a Tsige Shugaba Buhari-----Sarki Muhammad Sanusi II

Ya Kamata a Tsige Shugaba Buhari-----Sarki Muhammad Sanusi II
Sarki Sanusi ll

Ya Kamata a Tsige Shugaba Buhari-----Sarki Muhammad Sanusi II

Daga : Janaidu Amadu Doro.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta yi abin da za a tsige ta.

Sanusi ya ce kuɗaɗen da ake kashewa wajen bayar da tallafin mai sun isa abinda zai sa a tsige shugaban ƙasar.

Ya bayyana cewa, an biya miliyoyin kuɗaɗe da sunan tallafi ba tare da bin doka ba.

Sarkin ya ce a yayin da Najeriya ke kashe kuɗi akan man fetur, kasashe irin su Ghana da Rwanda sun mayar da hankali wajen kashewa Ilimi da harkar kiwon lafiya kuɗi.

Sanusi ya ce kuma majalissun tarayya na ji kuma su na gani amma ba sa yin abin da ya kamata.

Sanusi ya shahara wurin sukar duk wani abu da yake ganin ana yinsa ba bisa ƙa'ida ba, ba ruwansa da duk sukar da za ta biyo bayan matsayarsa.