Mi Ya Cire Faruku Yabo Daga Cikin APC Family?

Mi Ya Cire Faruku Yabo Daga Cikin APC Family?
Faruk Malami Yabo

Jagoran jam'iyar APC a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya godewa daukacin masu ruwa da tsaki da suka halarci gudanar da zaben shugabanni matakin jiha wanda ya gudana cikin lumana da kwatanta gaskiya.
A farko ya godewa Sanata Ibrahim A. Gobir da Sanata Salihu Bakwai. Sai tsohon mataimaki gwamnan Sakkwato Alhaji Ciso Dattijo da tsohon mataimakin gwamna Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto kuma Sakataren zartarwar asusun tallafawa rundunar 'yan sanda na Nijeriya da Bello Jibril Gada tsohon ministan Al'adu da yawon buda ido.
Ya jero 'yan majalisar tarayya 6 dake karkashin jam'iyar APC da 'yan majalisar dokokin jiha su 15, karkashin jagorancin Bello Isah Ambarura da tsoffin shugabannin majalisa Honarabul Umaru Shehu Goronyo da Lawali Labbo Margai, sai tsohon mataimaki shugaban majalisa Aliyu  Abubakar Tureta. Bello Muhammad Goronyo.
A rubutun jagoran ya godewa ministan 'yan sanda Muhammad maigari Dingyadi da tsohon minista Alhaji Yusuf Suleiman da tsoffin  'yan majalisar tarayya Honarabul Sa'idu Nabubkari da Aminu Sani Isa da Aliyu AA Shehu da Hassan Bala Abubakar da sauransu.
Sauran muhimman mutanen sun hada da Ambasada Abubakar Shehu Wurno da sahabi Isah Gada da Alhaji Bello Abubakar Wamakko da Garba Umar kyadawa da farfesa Garba Musa Maitafsiri da Alhaji Yusuf Goronyo da Alhaji Musa Bashar da AA Gumbi da Aliyu Oroji Wamakko(ciroman Wamakko).
Rashin ayyana sunan Faruku Yabo karara ya sanya Managarciya yin wannan tambaya mi ya cire shi daga cikin wannan 'Family'? 
Honarabul Abdullahi Hassan ya ce "Son rai ne kawai ya sanya aka yi haka, kuma shi Ambasadan yana nesa saboda lalurar aiki amma na tabbatar yana tuntubar Wamakko akai-akai ga harkokin jiha da suka shafi jam'iyar APC.
"Amma kwarai akwai mamaki a manta da wanda yake wakiltar Nijeriya a wata kasa kuma dan jam'iyar APC ba tare da an manta da wasu da ba su kai shi ba, yakamata wannan son ran a rage shi a APC Sakkwato matukar ana son samun nasara a zaben da ke gaba na 2023.

"In har Abdullahi Salame da Abubakar Gada jayayya suke yi tau shi Faruku mi ya yi?", tambayar da Abdullahi Hassan ya yi.