Bayan cire tallafin mai: Tinubu ya bukaci Majalisa ta amince ya ciyo bashin dala biliyan 8
Gwamnatin Tinubu ta rasa alkibla tun bayan da ta shigo a mulki take ta dambarwa neman mafita in da take ta kara jefa talaka cikin matsin rayuwa.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a ranar Laraba ya bukaci majalisar dattawan kasar ta amince ya ciyo bashin kusan dala biliyan 8 a wani bangare na sabon bashin ketare na shekarar 2022-2024 don yin ayyukan raya kasa da kiwon lafiya da ilimi da kuma tsaro.
Nijeriya ce kasar Afirka mafi karfin tattalin arziki kuma ita ce ta daya a hako man fetur, sai dai ta dogara ne a kan bashi saboda yadda ba ta iya tattara haraji da kuma yadda ta rage fitar da danyen man fetur zuwa ketare, wanda shi ne babbar hanyar da take samun kudin kasahen kasashen waje.
A wata wasika da ya aika wa majalisar dattawa, Shugaba Tinubu ya bukaci dala biliyan 7.86 da yuro miliyan 100, sai dai bai yi karin haske ba kan yadda za a samo kudin.
Gwamnatin Tinubu ta rasa alkibla tun bayan da ta shigo a mulki take ta dambarwa neman mafita in da take ta kara jefa talaka cikin matsin rayuwa.
Gwamnatin tajanye tallafin man fetur wanda shi ne kadai talaka a Nijeriya ke amfana da sunan gyara, daga nan kuma ta yi kurarin tallafawa ‘yan kasa don rage radadin janye tallafin mai abin da kwaliya ta kasa biyan kudin sabulu. Ana haka sai ga maganar neman bashi don yin aiyukkan raya kasa, abin tambaya anan su kudin da aka samu na tallafin mai mi za a yi da su.
managarciya