Mai shayi ya kashe ɗan shekara 20 kan zargin satar burodi a Jigawa
Rundunar ƴansanda ta jihar Jigawa ta kama wani mai shayi biyo bayan mutuwar wani matashi mai shekaru 20 da ya ke zargin ya lakada masa duka bisa zargin sa da satar burodi da madara da Indomie.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a garin Dutse na jihar Jigawa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce wanda aka kama din mai suna Abdulrashid Ya'u ya zargi mamacin da satar masa buirodi da madara.
Ya ce, wanda ake zargin ya daure mamacin mai suna Hassan Garba da igiya inda ya dinga dukansa da sanda har sai da yayi masa jina-jina.
Sanarwar ta ce, "A ranar 19/08/2024 da misalin karfe 05000hrs, bayanai daga mai garin Sararai na garin Jigawar tsada a karamar hukumar Dutse ya bayyana cewa, wani mai siyar da shayi mai suna, Abdulrashibu Ya'u mai shekaru 40 ya daki Hassan Garba mai shekaru 20 inda yayi masa jina-jina saboda zargin satar masa biredi da madara da man fetur.
" Bayan samun bayanan ne, tawagar jami'an tsaro ta isa wurin, inda aka kama wanda ake zargin da kuma kai wanda aka daka zuwa asibitin Rasheed Shekoni.
"Bayan isa asibitin, likitoci suka tabbatar da rasuwarsa".
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa a yayin da ake ci gaba da bincike.
managarciya