Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun buƙaci al'ummar musulmi na ƙasar su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah gobe Alhamis. Watan Dhul Hijja wanda ya kasance wata na 12 a jerin kalandar addinin Musulunci, shi ne watan da Musulman duniya ke yin Sallar Layya.
Ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024 za ta kasance daidai da 29 ga watan Dhul Qa'ada, bisa haka hukumomin Saudiyya suka nemi a fara duban watan 12.
"Kotun koli na kira ga ɗaukacin Musulmin ƙasar Saudi Arabia su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga gobe Alhamis, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1445AH daidai da 6 ga watan Yunin 2024.
"Ganin jinjirin watan ne zai tabbatar da ranakun aikin hajji da suka haɗa da ranar hawan Arfah da kuma ranar babbar Sallah."
Sanarwar ta buƙaci waɗanda za su iya duban watan da idanuwansu ko na'urar hangen nesa da su kai rahoton ganin watan ga kotu mafi kusa da su.