Dawo Da Tallafin Fetur: El-Rufa'i Ya Sa Zare Da Tinubu

Dawo Da Tallafin Fetur: El-Rufa'i Ya Sa Zare Da Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce tallafin man fetur ya dawo, amma yawancin ‘yan Najeriya ba su san haka ba. Da yake amsa tambayar manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a ranar Litinin, El-Rufai ya ce gwamnatin tarayya tana biyan kudin tallafi fiye da a baya. 

Ya yi nuni da cewa gwamnati ta ga cewa duk wani shiri na rage radadin janye tallafin ya gaza yin tasiri, wannan ya sa dole ta dawo da biyan tallafin, jaridar Daily Trust ta ruwaito. 

A jawabinsa na farko, shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana janye tallafin fetur, yana mai cewa babu wani alfanu a biyan talafin. 

Sai dai El-Rufai, wanda ya ce yana goyon bayan manufar janye tallafin, ya ce dole ne gwamnati ta yi gyare-gyaren da suka dace. “Janye tallafin man fetur wani kudiri ne da shugaban kasa ya aiwatar, kuma kudiri ne mai kyau. A koyaushe ina goyon bayan janye tallafin mai. 

“Amma a yayin aiwatarwa kamar yadda kuke gani gwamnati ta fahimci cewa dole ne a dawo da tallafin kuma a halin yanzu, muna biyan makudan kudade fiye da a baya." 

Jaridar Vanguard ta rahoto El-Rufai ya ce mutane da yawa ba su san cewa gwamnati ta dawo da biyan tallafin man fetur ba. 

"“Amma idan suna son sanin ko ana biyan tallafi ko ba a biya, sai su kwatanta farashin man fetur da dizal domin man fetur ya fi dizal tsada amma man dizal yana kan naira dubu daya yayin da man fetur ke kan N600 kan kowace lita. “Don haka har yanzu muna biyan tallafin man fetur saboda gwamnati ta fahimci akwai kura-kurai a yadda ta janye tallafin man da farko, dole ne a yi wasu 'yan gyare-gyare."