Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Sokoto ba Ta Biya Kudin Fansar Sarkin Gobir ba

Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Sokoto ba Ta Biya Kudin Fansar Sarkin Gobir ba

 

Gwamna Ahmad Aliyu ya yi magana kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar Sokoto, musamman a 'yan kwanakin nan da ake ta garkuwa da mutane. 

Mai girma Ahmad Aliyu ya ce tun a zamanin tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal aka samu wani gibi a yaki da 'yan bindiga, wanda ya ke kokarin cikewa. 
Hon. Nasir Bazza, babban mataimaki na musamman a kan kafafan sadarwa na soshiyal midiya ga Gwamna Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba. 
"Dole ne a nanata cewa sojoji ba su samu nasara a yaki da 'yan bindiga a lokacin Tambuwal ba saboda ba su da karfin da za su iya kai hare-hare a lokaci guda a dukkanin kananan hukumomin jihar. Da a ce gwamnatin Tambuwal ta kafa rundunar ‘yan banga, to da Gwamna Ahmed Aliyu ya samu abin da zai dora aiki a kansa. 
Sai dai, bai samu komai ba, dole ya fara daga tushe." 
Mai taimakawa  gwamnan ya ce gwamnatocin duniya ba wai na Sokoto kadai ba, ba sa biyan kudin fansa ko yin sulhu da 'yan ta'adda, saboda zai bude kofar da za a gagara rufewa 
"Da ace gwamnatin Sokoto ta biya kudin fansar hakimin da aka sace, da zuwa karshen shekara ta biya biliyoyi duk da sunan karbo mutane daga hannun 'yan bindiga. 
"Na farko dai hakan zai sa 'yan bindigar sun yi amfani da kudin wajen kara sayo makamai, kuma ba lallai ne su sako wanda suka tsaren bayan karbar kudin ba."
Hon. Nasir Bazza ya ci gaba da cewa, da ace gwamnatin jihar ta biya kudin fansar karbo basaraken, to da ta sabawa dokar yaki da ta'addanci ta Najeriya ta 2023. "Dokar ta haramtawa jihohi, iyalai ko abokan wadanda aka yi garkuwa da su biyan 'yan bindiga kudin fansa. 
Dokar ta na kokarin magance matsalar sace mutane da neman kudin fansa." kamar yadda kafar yada labarai ta Legit ta kawo.