Wani rahoto na nuni da cewa akwai akalla sanatoci 13 da har yanzu ke karbar fansho daga jihohinsu a matsayin tsaffin gwamnoni.
Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoto na Arise TV wanda ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel, ya nemi a dakatar da fanshon shi na gwamna tunda yanzu yana matsayin sanata a Majalisar Dattawa.
Gbenga ya aika da rokon ne cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 14 ga watan Yuni. A cikin takardar, gwamnan ya bukaci a dakatar da kudin fansho N676,376.95 (Dubu dari shida da saba'in da shida, da dari uku da saba'in da shida, da kwabo casa'in da biyar), na wata-wata da ake ba shi.
Sanatoci 13 da har yanzu ke karbar kudin fanshonsu na gwamna daga jihohinsu An tattaro jerin sunayen sanatocin da har yanzu ke karbar kudin fansho a matsayin tsaffin gwamnoni, da kuma albashinsu na Majalisar Dattawa kamar yadda Nigerian Tribune ta hada. 1. Godswill Akpabio (Akwa Ibom) 2007 – 2015 Godswill Akpabio ya rike kujerar gwamnan Akwa Ibom na wa'adi biyu a karkashin jam'iyyar PDP. Haka nan ya kuma rike ministan Neja Delta a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
A yanzu haka, shine shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ta 10.
2. Aliyu Wamakko (Sokoto) 2007 – 2015 Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi mataimakin gwamnan Sokoto na tsawon tenuwa biyu, wato daga 1999 zuwa 2006, kafin daga bisani ya zama gwamnan jihar daga 2007 zuwa 2015. A lokacin da yake gwamnan jihar Sokoto, ya mayar da hankali kan ababen more rayuwa, ilimi da bangaren lafiya a jihar.
Yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Sokoto ta arewa.
3. Abdulaziz Yari (Zamfara) 2011 – 2019 Abdulaziz Yari Abubakar tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya mulki jihar daga 2011 zuwa 2019.
A yanzu haka Yari shi ne sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya. Yari ya dauki hankula cikin 'yan kwanakinnan bayan fitowa da ya yi neman shugabancin Majalisar Dattawa.
4. Dave Umahi (Ebonyi) 2015 – 2023 Tsohon gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, na cikin sanatocin da har yanzu ke amsar fansho daga jiharsu.
Yanzu shi ne sanatan da ke wakiltar Ebonyi ta Kudu a Majalisar Dattawa karkashin jam'iyyar APC.
5. Aminu Tambuwal (Sokoto) 2015 – 2023 Aminu Waziri Tambuwal ya rike mukamin kakakin Majalisar Wakilai kafin rike gwamnan jihar Sokoto na tsawon tenuwa biyu.
A yanzu haka Tambuwal shi ne sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.
6. Adams Oshiomhole (Edo) 2008 – 2016
Adams Aliyu Oshiomole, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), kuma tsohon gwamnan jihar Edo na tsawon tenuwa biyu (daga 2008 zuwa 2016). A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa.
7. Ibrahim Dankambo (Gombe) 2011 – 2019 Ibrahim Hassan Dankwambo, shi ne sanatan da a yanzu haka ke wakiltar Gombe ta Arewa. Ya rike matsayin akanta janar na kasa a can baya, kafin zamansa gwamnan jihar Gombe daga 2011 zuwa 2019.
8. Abubakar Bello (Niger) 2015 – 2023 Abubakar Sani Bello ya yi gwamnan jihar Neja daga shekarar 2015 zuwa 2023. A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya.
9. Orji Kalu (Abia) 1999 – 2007 Orji Uzor Kalu tsohon dan siyasa ne da ya yi gwamnan jihar Abia daga 1999 zuwa 2007 karkashin jam'iyyar PDP. A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattaawa
10. Seriake Dickson (Bayelsa) 2012 – 2020 Henry Seriake Dickson tsohon gwamnan jihar Bayelsa ne da ya jagoranci jihar daga 2012 zuwa 2020.
11. Ibrahim Gaidam (Yobe) 2009 – 2019 Ibrahim Geidam shi ne tshohon gwamnan jihar Yobe da ya shugabanci jihar daga 2009 zuwa 2019. Shi ne sanatan da ke wakiltar Yobe ta Gabas a Majalisar Dattawa.
12. Adamu Aliro (Kebbi) 1999 – 2007 Muhammad Adamu Aliero, tsohon gwamnan jihar Kebbi daga 1999 zuwa 2007. Ya rike ministan Babban Birnin Tarayya a lokacin Umaru Musa Yar'adua. Yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
13. Danjuma Goje (Gombe) 2003 – 2011 Mohammed Danjuma Goje, shi ne tsohon gwamnan jihar Gombe da ya jagoranci jihar daga 2003 zuwa 2011. Goje a yanzu haka yana wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.