LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 21 da 22
"mai ne haka kakeyi Kabiru?daga ina kake?ba na hana kowa fita a gidan nan ba ta ina ka fita kai?"dai dai alhj Kml na ƙarasa maganarsa dai dai lokacin da Kabiru ya ɗauko wata zungureriyar takobi a kasan gadonsa tare da gariyo yayo waje yana ihu"sun taɓo mu!!"gaba ɗaya jikinshi tsuma yake kamar wanda yasha tsumi,
LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 21 da 22
Na
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
Not edited
*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*
P 21 & 22
Gida Baba ya shiga fuskarsa cike da annuri ya sanarwa da Mama abunda ke faruwa dan shi yanzu a tsarinshi yarinya indai macece ta daina karatu a gabansa secondary ma Allah yasa mata albarka,
Sosai Mama taji daɗin batun musamman ma da ya tabbstar mata da dangin mahaifinsu Khadee a cikin maganar,
Hayaniya ce ta haure a Gama dake nassarawa local government tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,ƴan daba ne ta ko ina saƙo da lungun uguwannin guda biyu Gama da Gawuna sosai suke rikin ba kama kafar yaro yayin da kowanne magidanci fatanshin ya isa ga mahallinshi,
sosai ƙurar taƙaddamar take tashi a tsakanin unguwan kusan kwana biyu kenan da faruwar hakan kuma yake kan faruwa ma,
a guje Kabiru ya shigo gidansu yana wani kalar ihu wanda kanaji kasan bana lafiya bane,gadangadan ya nufi ɗakinshi sai dai kan yakai ga ɗaukan abunda zai ɗauka alhj Kamalu ya fito daga ɗakinsa cikin firgicin jin ihunda Kabirun,
"mai ne haka kakeyi Kabiru?daga ina kake?ba na hana kowa fita a gidan nan ba ta ina ka fita kai?"dai dai alhj Kml na ƙarasa maganarsa dai dai lokacin da Kabiru ya ɗauko wata zungureriyar takobi a kasan gadonsa tare da gariyo yayo waje yana ihu"sun taɓo mu!!"gaba ɗaya jikinshi tsuma yake kamar wanda yasha tsumi,
"kai!kai!! ungo nan ja'iri kawai har wani rawar ƙafa kake saboda an taɓo ubanka to ba inda zakaje"alhj Kml ya faɗa yana yiwa Kabiru daƙuwa,
ƙaho aka busa a ta waje tuni duk wani ɗan taurin haye da na gado jikinshi ya fara ɓari suna fitowa da ɗaiɗai da ɗaiɗai,ganin wanki hula na neman kai Kabiru dare yasa cike da jarumta da dakiyar zuciya da kuma bushewa zuciya ya ingiza Mahaifin nashi dan ya fuskanci in dan ta shi ne bazai fita,yana in gizashi yayi gaba abunshi a 360o ya bar gidan,
Tashin hankali akace ba'a samasa rana hakanan alhj Kml ya faɗi warwas a ƙasa kuma Allah ya kawo tsautsayi,
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!"shine kalmar da Mahaifiyar Kabiru da kuma mahaifinsa alhj Kml suke maimaitawa domin tuni ƙashin hannunshi ya rabu da ɗan uwansa,
"hasbiyallah!"alhj Kml ya faɗa a fili lokacin da Mahaifiyar Kabiru ta ɗagoshi ta gyara masa kafun a hankali kuma tace"sannu,alhj ai laifinka ne sai kakewa yara tsawa"wani kallo ya bita da shi duk da a cikin ciwo yake,
yadda aka angizo ƙyauren ƙofar gidan ne yabawa kowa tsoro alhj Kml da ke zaune da tsatstsaman hannun da ya gama kumburewa ya ɗan leƙo dan ganin abunda ke faruwa,ga mamakinsa da Ahmad ƙanin kabiru yayi tozali yaron da zai haura shekara sha biyu ko sha uku ba ya shigo a ɗari uku da sittin ya haure ƴar gajeriyar katangar da akayi a farfajiyar gidan ya tsere,ko kyakkyawan second 20 ba'ayi da shigowarshi ba zugar ƴan daba ta shigo gidan,kan mai uwa da wabi suka saka kan kace mai sunyi ratata da mutanen gidan da gora anyiwa kowa walmakalifatu har ɗan karamin yaronsu da bai wuce shekara biyar ba,
a ɓangaren su Ameenatuh kuwa da naci da komai Khadeeja da Hammad suke kwaɗaita mata Abdallah tun bata wani bawa abun muhimmanci harta amince,aka sanya ranar biki wata guda,
mutanen Madinah kuwa tuni sukayi haramar dawowa gida Nigeria dan dama can asalinsu ƴan Nigeria ne faɗan mai tatsine da akayi a kano ne yasa Baba da yayanshi maɗaurin auren Umma yin hijira da komawa Niger kasantuwar su kaɗai iyayensu suka haifa kuma suka rasu yasa suka koma Niger tare,
Abdallah ne zaune da Ameenatuh ana shan ƙauna cikin tausayawa ya kalleta kafun yace"Hayaatie wai banji kina maganar zuwa dubiyar Abba ba,ko kunje ban sa ni ba, ba gayyata?"cikin mamaki ta kalleshi "wanne Abbah?" duban mamaki yake mata"kamar ya wanne Abbah Abba dai namu mahaifinku" tuni fuskarta ta canza dan Allah ya gani tana matukar son mahaifinta kawai dai ƙaddararsu ce ta raba su"ai ban sa ni ba,amma in sha Allah gobe da safe zamuje"saurin katseta yayi da faɗin "a'a naga Hammad yana nan kije ku fito ku duka har Khadeejan ya fa kwana biyu a kwance" tashi tayi yayi da can cikin tsokar jikinta ke mazari dan tanaso taje taga halinda Abbanta ya ciki "toh bari naje na faɗawa Baba" tana gama faɗa tayi ciki,
a falo ta samu Baba shi da Abba suna hira nan ta sanar masa sai dai shima tashi yayi yace fa shi za'a tafi,
motar Abba Baba ya hau shi da Khadeeja dan shi sunfi ɗasawa da ita saboda akwaita da saurin sabo da kuma surutu,yayin da Ameenatuh,Hammad da Abdallah suka fita a motar Abdallah,.
Sosai suka tausayawa Abba ganinsa a mawuyacin hali gaba ɗaya kamanninsa sun canza dama aka ce ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa,
ita dai Ameenatuh kuka kawai take dan Abba ya mugun bata tausayi,
kallo kawai Abba ke bisu da shi yana murmushi ya yafito Ameenatuh,cikin sanyin jiki ta je jikin gadon tayi masa sannu ya amsa yana kamo hannunta"Ameenatuh Uwar masu gida kinga yadda Allah yayi da ni ko,ba komai bane ke bibiyata face haƙinku ku da mahaifiyarku dan Allah ƴar nan ku yafe mun ku roƙamun mahaifiyarku ita ma ta yafe mun"ba Ameenatuh ba hatta Khadeeja da takejin haushinsa sai da ya bata tausayi bama tasan lokacin da hawaye ya fara fareti akan kuncinta ba,
"Bakomai Abba mu dama ba mu riƙe ka ba bama kayi mana komai ba in ma kayi mana mun daɗe da yafe maka"kallon Khadee yayi da ta makale jikin Baba tana kuka ita ma ya yafitota,a hankali ya maida dubansa ga Abdallah sai kuma ya fara kokarin mikewa Khadee tayi saurin dafe shi tana girgiza masa kai murmushi kawai yayi ya kara kai dubansa ka Abdallah yace"bayan hakkin iyalina kai me mutum na biyu da naci hakkinsa amma ina kara godiya ga Allah da yasa ban mutuba zan biyaka hakkin ka,kuma dama banyi amfani da su ba kawai hau ne da bakin duniya da kuma zugar aboki yasa na taɓa kayanka amma suna nan ko ƙuda bai taɓa ba kuma tun ranar da naganka da gudan jini na nasa amayar maka da abunka"a gogo Baba ya duba yace "kunga dare yayi ai anyi dubiya kuma Allah ya bada lada"ya maida dubansa ga Kml yace"kai kuma inaso ka bani takardar ƴata dan bana bukatar ta kara minti ɗaya masayin matarka sannan banaso ka dora mata idda "yaƙe Abba yayi kafun a hankali yace"tun ranar da ka bani umarnin sakar maka ƴa na saketa sai daya kuma na sauke mata idda ko yau ta samu miji tayi aure,ni ma nasan in naci gaba da rike auren Maryam na cika tantirin mara imani"....,
faka faka za'ayi a gama saboda gabatowar azumi
managarciya