WATA UNGUWA: Fita Ta 37
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
Bayan kamar sati ɗaya Maisha ta riga ta kafawa Jafsee tarkon da ba zai iya fita daga ciki ba. Ya amince da kamalarta har ya yi mata alƙawarin a sati na gaba zai zo birnin Balgori su ga juna kafin ya turo iyayensa a yi zancen aure.
Wata rana da yamma Jafsee yana ɗakinsu zaune tare da abokinsa Duddoo, lokaci zuwa lokacin yakan duba wayarsa da dukkan alama akwai wani abu da yake jira. Fuskarsa ta bayyanar da alamar damuwa.
Ya sake danna hasken babbar wayarsa tare da jan tsaki "Mtsww!"
Duddoo ya kalle shi, "Wai meke damunka? Tun ɗazu ina ta lura da kai duk ka wani sauya."
"Ka bari kawai mutumina, wallahi kiran masoyiyata nake jira tun ɗazu. Ga shi na yi ta gwada kira ta ƙi shiga."
"Wace masoyiyar taka kenan?"
"Haba abokina sabon kamun da na yi mana, Baby Mardee ina matuƙar sonta wallahi." Ya faɗa yana kallon Duddoo.
Duddoo ya gyara kwanciyarsa yana faɗar
"Allah Sarki! Yarinyar nan tausayi take ba ni, bata san ko waye kai ba da bata yi gigin shiga rayuwarka, domin a ƙarshe na san sai ka saka ta a damuwa fiye da wadda ka saka sauran 'yanmatanka na baya."
Ya wurga wa Duddoo harara "Me kake nufi?"
"Ina nufin ita ma yaudarar ta zaka yi kamar yadda ka yaudari Mahee a baya. Yarinyar da ta gwada maka ƙauna fiye da kowa da komai nata, ta bijirewa mahaifinta saboda kai? Amma daga ƙarshe ka wulaƙanta ta ka yi mata muguwar yaudara mai babbaka zuciya."
"Mtsww wai ya kake dawo mini da abin da ya wuce ne? Tabbas na yi nadamar yaudarar Mahee saboda daga baya ta dawo raina, na kuma ci bak'ar wuya a hannun kwalawa duk saboda ita, amma ka sani ita wannan yarinyar ta musamman ce a zuciyata aurenta ma zan yi."
Jin wannan zancen ya saka Duddoo ya juya masa ƙeya yana faɗar "Allah dai ya fidda A'i ga rogo."
Har ya buɗi baki zai sake cewa wani abu, wayar dake gabansa ta shiga ƙugin neman agaji, baki a washe hannu na kakkarwa ya damƙo wayar da ke ajiye akan karfet. Ya daga tare da kanga ta a kunnensa yana wani irin murmushi.
"Haba babyna ya zaki azabtar da ni da rashin jin muryarki na tsawon wuni ɗaya? Shin baki san cewa hakan zai iya illatar da lafiyata ba?"
Daga can ɓangaren Mardiyya ta kashe murya tare da ƙarya harshe ta ce
"Oh! Ka yi haƙuri yayana, hankalina ne ba a kwance ba, saboda Abbana ya kunno mini wuta, ya ce lallai idan kana ƙaunata da gaskiya sai dai ka zo ya ganka ku yi magana, son samu ma ka zo tare da magabatanka don a san matsaya akan zancenmu."
Ya ɗan muskuta ya ce "Kada ki damu in sha Allah za mu zo, zan yi ƙoƙarin shawo kan mahaifina har ya amince."
Ta ƙara rage murya cike da kıssa "Ya ce lallai idan ka wuce satin nan zai aurad da ni ga waninka, ni kuma ina tsoron na rasaka."
Ta ƙarasa zancen muryarta na rawa da alama tana gab da fashewa da kuka.
Cike da tashin hankali yake lallashinta "Ki yi haƙuri Mardee, ban taɓa ƙaunar wata ya mace kamar yadda nake ƙaunarki ba, ba zan bari na rasa damar aurenki ba. Bari na je na samu Babana tun yanzu domin da zafi-zafi akan daki ƙarfe."
Fatan samun nasara ta yi masa sannan ya miƙe ya kashe wayar cike da damuwa, har zai fice Duddoo ya ce "Ina kuma zaka je tun Beb ɗin ba su ƙaraso ba? Ko ka manta da deal ɗin mu na yau ne?"
Ya juyo yana jifar Duddoo da wani irin kallo kafin ya ce "Zan je gida na yi abin da yafi wannan muhimmanci, da auren nan ya tabbata na daina wannan harkar don ba zan juri bacın ran Mardee ba."
Ya fice a gaggauce ya bar Duddoo nan sake da baki, yana mamakin sauyawar abokin cin mushen na shi.
@@@@
Cikin sa'a kuwa ko da ya ƙarasa gida ya tarad da mahaifinsa, ya sanar da shi damuwarsa. Da farko baban bai ɗauki maganar da muhimmanci ba a cewarsa Shi ba zai je nema masa aure yanzu ba, gudun kada ya mayad da shi mutumin banza, ya je ya kuma yaudarar yarinyar mutane, ga shi ma ba shi da takamammiyar sana'a da ya tsayu a kanta.
Jin hakan ya saka Ja'afar Ya shiga lallaɓa shi tare da yi masa alƙawarin kwanan ne zai nemi sana'a. Sai a lokacin baban ya amince zai je. Ya nemi da ya kwatanta masa gidan.
Sai dai jin Ja'afar ya ambato sunan birnin Balgori ya saka baba ya kafe fur shi ba zai ci dogon zangon tafiya saboda yarinya ɗaya jal ba. Yarinyar da ma ko a hoto bai santa ba.
A nan Ja'afar ya nuna masa hotunanta da take turo masa ta dandalin sada zumunta na WhatsApp. Baba ya yaba da shigar kamalar da ke jikinta, sai dai duk da haka sai da aka kai ruwa rana kafin ya amince zai nemi abokin tafiya su je. Amma sai idan Ja'afar ɗin ne zai masu kuɗin mota.
Cike da farin ciki Jafsee ya amince, sannan ya fita cikin gari neman rancen dubu saba'in. Da ƙyar ya samo aro kuɗin, a cikinsu ne ya dinkawa babansa da ƙaninsa suturar da zasu saka idan za a tafi. Shi ma ya siyi wata dakakkiyar shadda ya ɗin ka. Suka fara shirin tafiya Balgori.
Cike da zumuɗi ya kira Mardee ya yi mata albishir da zuwansu tare da magabatansa nan da kwana biyu.
Ta nuna masa farincikinta tsantsa. Tana kashe wayar ta ce "Yes so! Tarkona ya kama kurciya. Allah Ya Yi mana yawancin ran gani."
Sai ta hau tiƙar rawa a gaban dressing mirror daga ita sai wani wando iya gwuiwa da ƙaramar riga da bata gama rufe mata cibiya ba.
Tana tsaka da tiƙar rawa ta dannawa wata lamba kira biyu a na uku ta ce
"Ina tafe da albishir mai daɗi, ku dai kawai ku tanadi kudadena ku ajiye mun."
Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta sake cewa "Jibi za su zo. Ku zama cikin shiri." Sa'annan ta kashe wayarta tana jin wani irin farin ciki na ratsa ta, har ta hango saukar Naira miliyan 10 a asusun ajiyarta. Domin ita bata raina arziƙi ko yaya ne.
Duk da kasancewarta gogaggiya a bariki kuma tana karɓar manyan kuɗi a hannun alhazzai, amma hakan bai saka ta daina yunwar kuɗi ba. Za ta iya yin aiki komai girmansa, kuma ta karɓi kuɗi komai kankantarsu. A cewar ta ƙari yafi ƙara kuma ai ko kogi ma ba ya ƙi daɗi ba...
@@@
A ɓangaren Irfan kuwa tun safe ya tashi cikin wani irin yanayi da ya kasa banbance na damuwa ne ko akasin haka. Hakan nan ya shirya ba walwala ya nufi office.
Can wuraren ƙarfe sha biyu na rana sakatariyarsa ta shigo ofishin tare da shaida masa cewa yana da baƙo a waje.
"Je ki ce ya shigo." Iya abin da ya faɗa kenan sannan ya ci gaba da rubutun da yake yi rai a jagule.
Buɗe ƙofar da aka yi ne ya saka shi ɗagowa karaf idanunsa suka sauka cikin na Hanif. A take yanayin walwala ya dirar masa. Cike da fara'a ya ce "Ah! Yaushe a gari mutumin? Kai sannu zuwa. Ƙaraso ka zauna."
Hanif yana murmushi ya zauna yana faɗar "Wallahi jiyan nan na dawo kuma gobe zan wuce Gigau, shi ne na ga ya kamata na biyo tanan mu gaisa."
"Ai kuwa wallahi ka kyauta sosai, to ya ka baro mutanen Balgorin?"
"Suna lafiya, Umar ma yana gaida ka."
Irfan ya yi Murmushi tare da cewa "Ba shi da kirki saboda haka ba zan amsa gaisuwarsa ba.."
Sai kuma ya yi dif kamar wanda ya tuna wani abu, nan da nan yanayinsa na ɗazu ya dawo.
A nan Hanif ke tambayarsa ko lafiya? Ya maida masa da cewa "Ina damuwa ne akan sanarwar neman matata da na sanya amma har yanzu shiru."
Hanif ya zazzaro ido, "kada dai a ce kai ne ke neman wata matashiya mai suna Maheerah da na ga ana haskawa a TV, lokacin ina Balgori."
"Wallahi ni ne, kasan ita zan aura, sai kuma ta ɓata. Amma a yanayin yadda ka tambaye ni kamar kasan wani abu game da ita."
Irfan ya faɗa yana tsare shi da kallon tuhuma.
Ganin cewa abokin nasa ya damu sosai da wannan zancen ya saka ya zaɓi ya faɗa masa gaskiyar abin da ya sani. Don haka ya kalli Irfan ya ce "Tabbas na yi tozali da wata mai kama da yarinyar da kake nema sak, sau biyu ina ganinta, sai dai zuciyata tana kokonton cewa ita ce ko ba ita ba ce."
Ya ɗan yi shiru yana kallon Irfan, shi kuwa Irfan da ma tun da suka fara zancen nan idanunsa na kan Hanif ɗin, don haka a ƙagauce ya ce "Ba ni labari, a ina kuka haɗu? Me ya saka kake kokonton ko ba ita ba ce?"
Hanif ya sauke ajiyar zuciya ya ce "A Balgori kuma haɗu kuma ko wacce haɗuwar tsautsayi ne ya haɗa mu. Haɗuwa ta farko ita ce ta fasa mini fitilar baya da motarta. Haɗuwa ta biyu kuma alhajin da ke jan motar da take ciki ne, ya buge mini madubin gefen mota kuma ya fito ya rufe ni da masifa."
Ya koma nisawa sannan ya ce "Abin da ya saka ni kokonto shi ne, wacce kake nema bata da jiki kuma kamilalliya ce. Ita kuma wacce na gani ta fi wacce ƙiba kaɗan, kuma tafi hasken fata sannan gogaggiyar 'yar bariki ce. Irin kayan da suke jikinta a dukkan lokutan da na ganta da yanayin da na ganta tare da alhajin bariki ya saka na tabbatar a raina cewa kilaki ce. Sai dai akwai wani abin da ya ɗaure mini kai kuma ya ba ni mamaki game da ita."
Irfan ya yi saurin cewa "Mene ne?" Domin tuni hankalinsa ya fara tashi, gabansa na tsananta bugawa.
'kada dai a ce Mahee bariki ta faɗa bayan ta bar gida?' ya faɗa a ransa.
"Abin mamakin shi ne, sananne abu ne cewa ƙadangarun bariki ba su da mutunci, ba su da kirki, za su iya taka kowa a lokacin da suka so suka ga dama. Amma ita wannan ta sha bamban da su, a lokacin da alhajin ya fito yana yi mini masifa, a maimakon ta ƙara zuga shi ko kuma ta zauna a mota ta yi kallo, sai ta fito daga motar tana cewa "Haba Alhajina, ba girmanka ba ne tsayuwa a nan kana ɗaga murya, mu ne muka ɓata masa mota wajibi ne a gare mu mu ba shi haƙuri." Sai ta maido dubanta a gare ni tare da saka hannu a jakarta ta ɗauko bandir na ɗari biyar-biyar ta miƙa mini tana faɗar "Don Allah ka yi haƙuri bawan Allah! Ga wannan ka gyara ɓarnar da muka yi maka."
Tana gama faɗa ta saƙala hannunta a jikin nasa suka juya zuwa mota tana lallashinsa shi ko sai cika da batsewa yake. Wannan ne abin da ya ɗaure mini kai game da ita, lallai ya kamata ka je can ka bincika mai yiwuwa wacce kake nema ce yanayin rayuwa ya dawo da ita haka."
Yana gama faɗa ya miƙe ya yi wa Irfan sallama, amma kafin ya tafi sai da ya kwatanta masa wuraren da suka haɗu sannan ya ƙara da cewa "Idan kana buƙatar wani ƙarin taimakon game da bayanan can ka nemi Umar, na san zai taimaka maka. Allah Ya tsananta rabo." Daga haka ya saka kai ya fice daga ofishin yana tausayawa abokinsa, haƙiƙa soyayya na wahalar da shi.
UMMU INTEESAR CE