KANWATA: Fita Ta Biyu
KANWATA
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 2*
*Free book ayi comment da share pls*
~Mama ganin ranta ne zaici gaba da b'aci yasata barinsu ta shige d'aki, Fadila mikewa tayi taje wurinda Amrah ta zauna tana kuka, Janyota tayi jikinta tana cewa "sannu kinji ciwo ne?"
Amrah shiru tayi tana kallon Yayarta yanda ya rud'e akanta bayan itace ma Mama tafi dukanta, far far tayi da idonta tace "ai dama idan ana dukanmu to b'uya nakeyi a bayanki bulala baya tab'ani sosai, kinsanni da tsoron bulala"
Dariyan farin ciki Fadila tayi "naji dad'i tunda bulalan bai tab'aki sosai ba"
Amrah kasa tayi da murya tace "nagodewa Allah daya bani Yaya wacce take sona fiyeda kanta, Adda ina matukar sonki kamar yanda kema kike sona, Bazanso mu rabu dake ba"
Rungumeta Fadila tayi "ki daina maganar Rabuwa Amrah, Auren nanma wallahi zan iya fasawa domin samun farin cikinki"
Mama ce tafito daga d'aki, kallon Takaici tayiwa Fadila tace "lalle Fadila bakida hankali, zaki fasa Aurenki? To idan kin fasa Aurenki itama Amrah kenan haka zata zauna? Sai kuyita zama min a gida da zarar nayi wanka Ku zubamin ido ko? Tofa baki isa ba Fadila, babban kuskuren da zakiyi shine kisa a fasa Aurenki, zakiga bakin ciki ranan, kutashi maza kuyimin wanke wanke"
Fadila tace "ni zanyi wanke wanken Mama, ita Amrah zata gyara mana d'akinmu" tafad'i hakane don tasan d'akinsu a gyare yake idan Amrah taje saidai kawai ta kwanta.
Mama batayi musu magana ba, kawai tashiga kitchen, Fadila tashi tayi tafara wanke wanke ita kuma Amrah kwanciyarta taje tayi a d'aki tanajin dad'in irin so da Yayarta take nuna mata.
"Kamal da Maman shine sukazo da yammacin ranar, Zobe me kyau Kamal yasawa Fadila a hannunta Tafi akayi musu, Maman Kamal ce taciro wasu lafiyayyun Leshi guda biyar ta baiwa Fadila, Fadila aunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tace "nagode Umma"
Maman Kamal kallonta tayi tanajin son yarinyar yana kara shiga zuciyarta, "karki damu 'Yata kidaina godemin"
Fadila dukar da kai kawai tayi, Amrah ce tafito da Pure Water a hannunta, mikawa su Kamal tayi, karb'a yayi yana dariya yace "kaga matar d'an kauye"
Murgud'a baki tayi tace "eh d'in"
Fadila dariya kawai sukayi, an gama baiko kowa ya watse, Fadila ce ta baza kayan da Maman Kamal tabata a cikin gida, kiran Amrah tayi tace "zoki zab'i duk Wanda yayi miki kyau a ciki"
Amrah kawar da kanta tayi gefe tace "gaskiya Adda nikam bazan iya sa kayanda Maman Kamal takawo gidannan ba, sabida da kud'in Zina ta siyesu"
Fadila waro manyan idonta tayi tace "Amrah me kike fad'ane haka? Kinada tabbacin tanayin Zina ne? Zatofa zunubi ne"
Amrah tab'e baki tayi tace "ai ni da idona na ganta da Alhaji Mamman me zinari, kuma duk garinnan waye baisan shi d'an iska bane d'an kawali"
Fadila tayi shiru tana mamaki, Mama na zaune a gefe tana jinsu da gangan takiyin magana tana jiran taji me Fadila zata fad'a.
"Shikenan Kanwata idan ke bazaki sa ba to nima banaso, mu siyar ko kuma mu kyautar, hakan yayi miki?"
Amrah saida tayi tunani kafin tace "eh yayi min"
Mama ce wacce taji ranta ya b'aci ta taso tazo wurinsu, zare manyan idonta tayi tace "ke Amrah Amma bakida tausayi kuma bakida tunani, kinsan yanda Fadila takeson Kamal duk kyautar data shigo idan ta hannunshi ne dolene taji dad'inshi, Amma ke kina amfani da yadda take sonki kina cutar da ita"
Fadila ce ta d'ago kanta tace "mama wani irin magana kikeyi haka? Amrah ce zata cutar dani? Gaskiya fa take fad'amin batason na hallaka ne shiyasa, Amma Mama Dan Allah kidaina fad'an haka"
Amrah tashi tayi a wurin ranta a b'ace ta wuce d'aki, Fadila tace "Mama kingani ko? Gashi yanzu daga fad'an gaskiya an b'ata mata rai, tashi tayi itama tashige d'aki tana baiwa Amrah hakuri, sukabar Mama tsaye tana ganin ikon Allah, da kyar Fadila tasamu Amrah ta hakura, haka suka siyar da leshin gaba d'aya.
"Yau takama ranar laraba, su Amrah sunada Walima a islamiyyar su, Dugayen Riga sukasa itada Fadila rigan komai nashi kala d'aya kwalliya sukayi me kyau, sunyi kyau ba wasa, Fadila tadafa abincin Walima wa Amrah, flasks d'aya kowa ya rike a hannu Fadila tarike babban na shinkafa ita kuma Amrah tarike karamin na Miya, sunyi kyau kamar ka sace ka gudu, Kamal ne yazo yayi parking na motarshi, shiga sukayi suka rike abincin a cinyarsu, Fadila amaikon ta zauna a gidan gaba, sai tace wai idan ta zauna a gaba kanwarta zatayi zaman kad'aici a baya, Kamal juyawa yayi yana kallonta yace "nan da islamiyyansu shine zatayi zaman kad'aici?"
"Eh" shine Amsar data bashi, Amrah tace "Adda nikam babu wani zaman kad'aici kawai dai kije ki zauna"
Fadila Sam taki zaman duk yanda sukayi da ita, Shikuma Kamal yace idan suka zauna a baya dukansu tofa za'ace shi driver d'insu ne, daga karshe Fadila tace "saidai Amrah ta zauna a gaba"
Amrah ganin zasuyi latti kuma gashi tana daga cikin wad'an da zasuyi karatu yasata bud'e motar tashiga gaba ta zauna, fira sukeyi da Kamal tana bashi labarin yarantarsu itada Fadila, sai dariya Kamal yakeyi ita kuma Amrah ta zage tanata surutu, Fadila sai murmushi kawai takeyi tana jin dad'in kanwarta da Wanda take so a rayuwarta suna dariya, abun ba karamin burgeta yayi ba, har suka iso Wurin walimar, Amrah ce ta d'auko flasks d'in duka biyu tashige cikin islamiyar dashi, Fadila ce ta koma gaba ta zauna tana dariya, a hankali suka fara firan su na masoya wad'anda suka jima suna son junarsu, Fadila ji takeyi idan bata Auri Kamal ba komai zai iya faruwa da ita, shima Kamal jin Fadila yake a cikin zuciyarshi "Kamal ina sonka, Dan Allah kada ka gujeni a kowani hali"
Kamal rufe idonshi yayi yanajin soyayyarta a zuciyarshi bud'e bakinshi yayi tareda idonshi ya zuba mata, itama kanta ta d'ago tana kallon cikin idonshi, wani sako suke turawa juna ta cikin idanunsu, Fadila ce tafara saukar da kanta kasa cikin muryanshi me sanyi da kuma dad'i yace "Ina sonki nima my fiancy, idan kinga ban Aureki ba, to saidai idan nadaina numfashi, mutuwace kad'ai zata rabamu itama ina addu'ar ta d'aukemu lokaci d'aya"
Fadila rufe idonta tayi tanajin wani yanayi a jikinta, cikin sanyin muryanta tace "ka daina maganar mutuwa yanzu sai munyi Aure mun haifi yara" tana fad'an haka ta rufe fuskarta da hannayenta biyu alamar taji kunya,
Dariya Kamal yayi yace "ki bud'e fuskar mana ai gaskiya kika fad'a kodai kinajin kunyata ne yau?"
Fadila bud'e motar tayi ta fice da gudu, Kamal sai dariya yake da karfi yace "idan kun gama ki kirani zanzo in d'aukeku"
Fadila bata juya ba kuma tajishi, motarshi yaja yayi tadiyarshi yanajin farin ciki, a duk lokacin da Fadila tayi Abu farin ciki yake sashi.
"Amrah sunyi Walima tayi karatun kur'ani itace tazo number 2 sun samu gift me yawa, Fadila ce tajata gefe tabata wani Abu acikin kwali tace "congratulations ga gift nawa"
Amrah bud'ewa tayi taga wata lafiyayyen waya spark 3 sabo dal, tsalle tayi ta rungume Fadila tana jin dad'i, Fadila ma rungumeta tayi tace "kibi wayar a hankali domin yanzu waya yana lalata 'yanmata"
Amrah dariya tayi tace "insha Allah Adda zan kiyaye"
Fadila ce takira Kamal tace sun gama, ba jimawa shima ya karaso suka shiga motar, a hanya yace "number nawa kikazo Kanwa ta?"
Amrah cikin murnar wayar da Fadila tabata tace "number 2, kaga har Adda tabani kyautar waya sabuwa dal" ta Ciro wayar ta nuna mishi,
Murmushi yayi yace "ai baki dace da wannan wayar ba kamata ace burin kwaila tasiya miki ko"
Amrah turo baki tayi tace "saika kwace ai d'an bakin ciki kawai"
Dariya yayi yaciro wata sabuwar Leda babba yace "nikuma ga gift d'in danayi miki"
Mika mata yayi, yakuma Ciro irinshi ya mikawa Fadila yace "fiancy kema ga naki" Murna sukayi gaba d'ayansu sukayi mishi godiya, yana dropping Nasu yatafi basuyi wani fira sosai ba,
Fadila da Amrah suna shiga gida suka bud'e ledar, na Amrah wani kwalin wayane kiran Samsung shigen na hannun Fadila Amma na Fadila yafi nata fad'i, sai turare kala biyu manya masu kamshi, sai kwalin chocolate da sweet Leda d'aya, murna tayi tanata jin dad'i, Fadila ma bud'ewa tayi taga wani babban kwalin biscuit Wanda aka fitar da shape d'in kwalin kamar heart, sai turare itama guda biyu da kwalin chocolate, tayi murna sosai itama, fita sukayi da kayan sukaje d'akin Mama, lokacin Mama tana kwance akan Sofa sai Abba daya kwanta shima a gefe d'aya, Amrah ce tace "Mama Abba kunga gift Dana samu yau kuwa?"
Abbane ya mike yace "idan banda abinki tayaya zamu gani baki nuna mana ba Amrah"
Amrah washe baki tayi tashigo da kayan duka ta nuna musu, Kallonta Mama tayi tace "yanzu wani wayan zaki rike, na yayarki ko kuma na Saurayin Yayarki?"
Amrah kallon Mama tayi tace "Mama ai na Yaya Kamal yafi girma da kuma kyaun camera shi zan rike kinga saimuyi anko da Yayata ko?"
Fadila ce tace "eh mana ki rike nashin yafi kyau kuma zamuyi anko"
Mama ce tayi dariya tace "Allah yayi muku Albarka yarana"
Suma suka Amsa da "Amin"
Abbama Addu'a yayi musu, sun Amsa suka kwashe kayan suka tafi.
_Washe gari_
Kamal ne yakira Fadila a waya "hello fiancy"
Fadila tace "na'am fiancy"
"Dama nakiraki ne don in sanar dake yau Ummana zasuzo asa ranar Aurenmu"
Murna Fadila tayi tace "da gaske?"
Kamal yace "aa da wasa ne"
Dariya tayi tace "gaskiya yau ina cikin farin ciki"
Shima dariya yayi yace "nima haka tin d'azu sai murna nake, kishirya anjima zamuje wurin shan ice cream"
Fadila "yawwa dama najima banje ba"
Sallama sukayi yace mata "I love you"
Itama Fadila tace "I love you too"
"Adda naji kamar kuna maganar sa rana"
Fadila kallon Amrah tayi cikin farin ciki tace "yau za'azo ayi gaisuwan Aurenmu da Kamal, ina cikin farin ciki Amrah"
Amrah dariya tayi itama cikin farin ciki tace "bari inje kasuwa anjima zan fitarda anko, sabida kawayena dayawa sunce sunaso".
_Jiddah Ce....
08144818849
managarciya