WATA UNGUWA: Fita Ta 21

WATA UNGUWA: Fita Ta 21

BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

 

 

DAWOWA DAGA LABARI.

 

 

 

A yan kwanakin nan Biba ta fara laulayi da alama tana ɗauke da ƙarami ciki. Habibu da ya kasa gane kan ciwonta ya ɗauke ta zuwa Asibiti a gwajin farko aka gano tana ɗauke da cikin wata uku. Murna a gun Habibu abin ba ya faduwa yake tamkar ya taka kan jariri. Nan fa ya shiga bata kulawa ta musamman domin ya rage cika dare a kasuwa sai ya dawo tun kafin magariba. Hakan ya damu Biba sosai duk jinta take a tauye, shi ya sa ta matsu ya daina dawowa da wuri domin duk ya takura mata ga shi ƙazantarta ta daɗu tun da ta fara laulayi, shi kuma ya tsani ƙazanta yana da matuƙar tsafta da son ƙamshi shi ya sa kullum yake faɗa da Biba.

 

Watarana ya dawo gida wuraren 6pm ya tarar da gidan a kazance kamar bolar cikin gari. Tun daga ƙofa ya fara ƙwala mata kira.

 

"Nona! Biba! Habiba!!" Da ƙarfi kamar zai fasa bangon gidan.

 

Ta fito a tsorace tana maida numfashi "Haba maigida, wannan kiran kamar zaka fasa min dodon kunne? Duk ma ka tsorata ni wallahi."

 

Ya harareta, ta numfasa ta ce  "Ba don Ni ba ko don yaronka dake ciki ai ka sassauta kasan ba a son mai ciki tana tsorata zai iya shafar lafiyar yaron dake jiki."

 

Kalamanta sun sanyayar masa jiki domin Allah ya jarabce shi da son yara, ga shi tun daga kan Salmah yau shekara biyar kenan ba su kuma samun haihuwa ba sai yanzu da suke saka rai, don haka ya wuce ta zuwa daki ba tare da yace komai ba.

 

Ta same shi a cikin ɗakin ta zauna tana murmushi "Ka yi haƙuri ban faɗa don na bata maka rai ba."

 

"Ya wuce." Ya faɗa a tsaitsaye.

 

Ta ƙara wadata fuskarta da murmushi "Ka dan yi murmushi mana."

 

A maimakon ya bi umurninta sai ya ƙara yanke fuska ya ce "Don Allah Biba sai yaushe zaki gyara ki daina ƙazanta? Da can lokacin da muka yi aure ai ba haka kike ba, me ya canza ki?"

 

Cikin yanayin damuwa ta ce "Ka yi haƙuri ayyukan ne ke mun yawa, ga kula da yarinya ga aikin gida da girki shi ya sa, da can kuwa ban da kowa. Amma Insha Allah zan gyara."

 

Sai a yanzu ya sake fuskarsa ya ce "Ko kefa, ki tuna Habiba yar gayun dana sani ada ina so ki dawo ita."

 

Ta masa murmushin yaƙe a ranta ta ce 'Masifafe, Allah Ya nuna min randa zaka daina dawowa da wuri.'

 

A fili kuwa cewa ta yi "Am maigida wai yanzu babu customers ne da yawa kamar da?"

 

"Me kika gani?" Ya waigo yana dubanta.

 

"Na ga ne ka daina kaiwa dare kamar da."

 

Ya fadada murmushinsa ya ce "Akwai customers sosai fiye da da, ina dawowa da wuri ne don baki kulawa ta musamman saboda wannan." Ya nuna cikinta.

 

"Kai ai kuwa na gode, amma duk da haka, ya kamata ka dinga tsayawa har 9 ko 9:30 don na lura cinikin daren ya fi tafiya, Ni zan aika gida ƙanwata ta zo ta dinga taya ni ayyuka ka ga shi kenan." Ta faɗa tana murmushin yake.

 

Ya amsa mata da "To zan duba, bani abincina."

 

Ta tashi ta miƙo masa abincinsa ya janyo Salmah kusa da shi suka ci tare.

 

Bayan wani ɗan lokaci Habibu ya ci gaba da jimawa a kasuwa, Biba kuma ta ci gaba da Sabgoginta na yawace-yawace.

 

A gefe ɗaya takan aiki Salmah gidan Baba mai itace sayen wani abu irinsu daddawa, Maggi da sauransu. Inda shi kuma Baba mai itace ya yi amfani da damar ya ci gaba da lalata mata yarinya ba tare da ta sani ba. Duk lokacin da Salmar ta yi yunƙurin sanar da ita, sai ta kwatse ta bata bari ta yi magana.

 

Bayan watanni Shida Biba ta haifi ɗanta kyakkyawa, murna wurin Habibu ba a magana yau dai ya samu Magaji Namiji.

Ranar suna yaro ya ci sunan Salman, a gidan yaya Hanne aka yi shagulgulan suna kasancewar ita gidanta ba ya da girma sosai.

 

A haka Biba ta ci gaba da renon yaronta cikin kulawa da taimakon matar babanta har zuwa lokacin da ta yi arba'in. Bayan wasu watanni Habibu ya bijiro da zancen ƙara aure. Nan fa Biba ta tuma tara bata taɓa ƙasa ba, ta ƙeƙashe ido kan cewa bai isa ba.

 

Watarana ta same shi zaune a falo yana rungume da Salim ta tsaya a kan shi ƙiƙam.

 

"Habibu ni fa ban fahimcin wannan abun ba? Duka duka yaushe ne muka yi auren da zaka tsiro wata maganar banza? Me ka rasa a rayuwar aurenka da ni da har wannan tunanin ya shige ka?" Ta faɗa tana ta huci kamar macijiya.

 

Bai tari numfashinta ba, sai da ya bari ta gama sauka sannan ya ce "Na rasa tsafta a gidana, ba kya kulawa da yarana yadda ya kamata  ni kaina bana samun kyakkyawar kulawa da ta dace, me yasa ba zan yi tunanin ƙarin aure ba?" Ya kalle ta a ɗage.

 

"Haka kace?"

 

"Eh haka na ce." Ya mayar mata.

 

Ta juya tana jan tsaki tare da faɗar "Ayi mu gani idan tusa zata hura huta."

 

"Zata hura kuwa har ma ayi sanwa akwashe a ci." Ta tsinto muryarsa yana faɗa yayin da ta je kofar shiga uwar ɗaka.

 

Tun daga lokacin ne kuma kwanciyar hankali ya ƙauracewa gidan, Biba ta daina kula Habibu sam, ko abinci ta yi bata ajiye mishi sai dai ya dafa nasa ya ci. Da ya gano cewa da gayya take yi masa wannan abubuwan sai ya dinga ciko cikinsa daga kasuwa. Da ya shigo sai dai ya kwanta ya tashi, shi ma kwanan gidan bisa tilas yake yinsa domin ji yake tamkar a ƙaya yake saboda kazantar matar tasa ta ninku, har kayan miya take ajiye wa akan gado in ta ga dama.

 

Sai dai duk da hakan Habibu bai fasa shirinsa ba, bai kuma sake faɗa mata komai ba, sai ana gobe za'a daura auren da dare ya same ta a ɗaki, ya jefa mata invitation card a jiki.

 

"Gobe za'a ɗaura mini aure da yar shilar amaryata yar gayu, idan kin ga dama ki gyara gidan in baki gani ba kuma matsalar ki, domin ke za'a zaga ba ni ba." Yana gama faɗa ya fice daga ɗakin zuwa banɗakin dake tsakar gida.

 

Nan ta saki baki galala, ta bi shi da kallo har ya ɓulle. Sai ga shi hadarin da ya gangamo daga idanunta ya fara zubar da ruwan ƙwalla.

 

Tana jin motsintsa ta yi saurin share fuskarta tare da gayyato jarumta a zuciyarta ta ce "A'ina zaka ajiye matar? Ko a gidansu zaku tare?" Tana yar dariya irin ta takaicin nan.

 

"Wannan ba matsalarki ba ne, ko da yake akwai haƙƙin maƙwaftaka bari na faɗa miki." Ya yi murmushi sannan ya ƙulla zancensa da faɗar "Shalelena zata tare ne a sabon gidan dana gina mana, tun da na lura wacce na yi ginin don ita ba zata iya kula da shi ba."

 

Ji ta yi tamkar yana watsa mata ruwan zafi amma ya ta iya? Akan tilas ta haƙura, kasancewar dare ya riga ya yi, idan ma tace zata fita yanzu to ina ta dosa? Tana neman wanda zai bata shawarar da zata fisshe ta a wannan lamari, sai dai _bakin alƙalami ya riga ya bushe._

 

Washegari da misalin ƙarfe takwas na safe aka ɗaura auren Habibu da Amaryarsa Safiya akan sadaki Naira dubu hamsin.

 

Bayan Amarya ta tare Habibu ya ci gaba da shariya da lamarin Biba sai dai ranar girkinta zai zo ya kwana, tun da safe zai fita ko magana ba ya yi mata da ta gaji ita ta nemi sulhu da kanta.

 

Bayan wata ɗaya da auren Habibu wani mummunan al'amari ya faru, domin Salmah ce ta fara wani ciwo da ba a gane kanta ba. Gata ƙanƙanuwar yarinya amma wari take yi, saboda matsalar da ta dame ta ba abinda take yi masu sai kuka tana nuna gurin da ke mata azabar.

 

Lokacin shigowar Habibu gidan kenan,ganin yadda uwar ta share ta ya saka ya matsa kusa don duba abin da ke damunta.

 

Da hanzari ya ja da baya yana tsattsaro ido tsikar jikinsa na tashi, cikin Muryar tashin hankali ya ce "Tsutsotsi a jikin 'yata? Wannan wane irin mummunan ciwo ne?"

 

Shin menene ya samu Salmah? Ya zata kaya tsakanin Biba da Habibu bayan ya gano sakacinta ne ya lalata mutuncin yarsa?

 

 

 

Ummu inteesar ce