LISSAFIN ƘADDARA; Fita Ta 19 & 20
LISSAFIN ƘADDARA
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
Not edited
*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*
P 19 & 20
a fili Abban Ameenatuh yace"tab ashe Baban Mairona babban kai ne,to wallahi bazan saketa sai dai ayi tsiyar domin kuwa ai ba cewa nayi bana sonta ba"shi dai Baba yariga yayi gaba kuma sarai yaji maganar Kamalu kawai dai yayi kunnen uwar shegu dashi kuma yaga alamar baiso maganar tafito ba,
9:20pm a Briget tayiwa Abban Ameenatuh,ya aika yaro gidan Alhj Sabo akan yayi masa iso da shi,ba a ɗau lokaci ba sai ga Sabo fuska fuska a haɗe kamar kunun kanwa,ko sallama Kamalu bai samu arziƙinta daga wajen Alhj Sabo ba,ƙiƙam ya tsaya gaban Abban Ameenatuh kamar sabon dogare sai wani ɓata fuska yake,ganin wankin hula na neman kai su dare yasa Alhj Kamalu cewa"wai kai ciccin maganin mai kake ko wani abu ya faru ba tare da sa ni na ba ne?"ya ƙarasa maganar da alamun tambaya,kallon banza alhj Sabo ya watsa masa kafun ya samu ariƙin yi masa magana cikin ɓacin rai "wato kai Kamalu rashin darajar taka har akaina zaka gwadata?,kai kasan nasank ciki da waje wallahi duk wani hau ɗinka a tafin hannuna nake kallonka"ya karasa maganar yana tura tunbi gaba,shima alhj Kamalu kallon banzan ya watsa masa kafun yace"a'a dai kawai dai kasan wanda ka sa ni malam amma ni nafi ƙarfin sa ninka kaima ka sa ni shakundum nake nafi karfin kai ka raina ni,wai ma to mai nayi maka ne dakake fama wannan hanƙoron?"can gefe jikin dakalin gidan alhj Sabo ya matsa ya zauna dan baya jurar tsayuwa haka alhj Kml ya bishi shima ya zauna "kafi dan dako sa nin yasha Kml,ka rigada ka bani yarinya wato shine zaka haɗa ni da wannan yaro dan na bar maka ɗiyarka sannan kuma ka gudu ka bar ni a wajen, sarai kasan na fika gogewa Malam ba sai abun ya kai ga haka ba ka bani kuɗina wannan Ameenatuh ko gwalce na haƙura da ita,haba yarinya tun kan takai haka kake cimun kuɗi shine yanzu ka ɓullomun ta bayan gida ka turomun wannan yaro ko,to wallahi duk wani kuɗi da kasan na baka da sunan wannan yarinya ka tattaromun na fasa ga ƴammata nan indai kana da kuɗi sai wacce ka zaɓa"yaja maganar yana haki dan da kyar ya kai aya kuma ya nace sai yakai ayar,
Dariya sosai Kml yayi harda su riƙe ciki kafun kuma yasha kunu irin ba mutuncin nan yace"kai tunaninka har akwai wani kuɗi da zaishiga hannuna ya fita ba tare da dalili ba,to in ma kana tunanin haka tun wuri ka canza dan wallahi na ci kuma naci banza,kuma kai ƙaramun tantirine bari ma na baka labari"sai da ya tulluƙe da dariya kafun ya ɗora da "ɓarauniyar ƙanwarka da k haɗi da ita kancewa ita uwar mazace,naji uwar mazace dan kuwa ƴaƴa har uku ta haifamun kuma duk maza sai dai wani hanzari ba gudu ba ai dama baka faɗamun ƴar uwarka ɓarauniya bace kuma zata haifarmun ɓarayi ba dan haka naji daɗi da Allah yasa ɗanka ya gwada akan dukiyarka domin kuwa kuɗin aure da ka bayar ɗan ƴar uwarka kuma ɗan amininka ya sace dan haka ni bazan ɗau asara ba sarai kuma kasani" yana kaiwa nan yayi gaba abunsa yanaji alhj Sabo na kwala masa kira yayi biris dashi,
Khadeeja ce kwance jikin Ameentuh tana mata tsifa dan yau alhamis ba islamiyya,shigowar Hammad ɗakin bakinshi ɗauke da sallama ne ya katse musu ƴar hirar da sukeyi"wai ke komai sai anyi miki bazaki iya komai da kanki ba,haba kin fiye son jiki wallahi"hararar wasa Ameenatuh ta aika masa kan cikin muryarta mai taushi da sanyi tace"kyaleta lokacinta ne watarana sai labari"ai tun kan ta ƙarasa Khadeeja tace"haba dan Allah bawan Allah kafiye samun ido komai kaga sister tayi mun sai kayi magana,wai kai bakason ta wahala to in ma wani abune a zuciyarka ka cire dan ɗazuma wanda zata aura yazo"bige mata baki Ameenatuh tayi cike da takaicin Khadeejan ta fara mata faɗa "ni fa Khadee bana son faɗi ba'a tambayeki ba kekuma naga kwanan nan gigi ne akanki,ki kiyaye ni kafun na fara saɓa miki wallahi da ai ba haka kike ba"ta ƙarasa maganar fuskarta ba walwala dan Allah ya gani ita bata iya faɗa ba,turo baki Khadee tayi kafun cikin shagwaɓa tace"dama can yunwa ce ai take hanani magana,kuma ni wallahi banga wa ni aibun Abdallah ba"tsaki Hammad yayi yana makawa Khadee harara kafun cikin wasa shima yace"malam ana magana da manya karki ƙara sa mana baki dan kinga baiwar Allah tana da farin jini ko shine kike baƙin ciki,to kema ki daina wannan masifar kiga tuni zakiga kema ana miki go slow"baki kawai Khadee ta tura gaba jin yadda Ameenatuh ta matseta kafun ta tashi tana karkaɓe jiki tace"Ya Hammad zo ka ƙarasa mata dan Allah zanje Mama tana kirana mantawa nayi tun ɗazu"tashi yayi yana bin bayanta yace "Allah ya kiyaye ina da abunyi"nan kuwa ya ƙara tunzura Khadee ba damar magana sai dai tura baki gaba,ɗan dawowa baya yayi kaɗan ya sakar mata murmushi sannan ya raɗa mata "kiyi biyayya ko na taimaka miki nace ina sonki yarinya"kuka ta fara tana tirja ƙafa a kasa kallonta kawai Ameenatuh tayi ta girgiza kai dan bata ji abunda Hammad ɗin ya faɗa mata ba"kinga Deeje dan Allah banason sakalci kiyiwa mutane shiru"ta juyo ga Hammad "kai kuma dan Allah muje kawai baka lallaɓata ba zakasamun ita kuka,kai haka akace maka ana fadanci,to wallahi ka lallaɓata in naga kamun ludayinka na taimaka maka na baka it..""Allah ya kiyaye wannan baƙin mai zanyi da shi ke dai ya lallaɓaki"dariya sosai Hammad yayi sannan ya kama hannun Ameenatuh sukabar ɗakin dan ya fuskanci Khadee akwai rigima,
a falon Mama suka sameta ita da Umma suna hira abun har mamaki yake bawa Ameenatuh ta yadda basa gajiya da hira,
guri suka samu suka zauna ita da Hammad,kafun Mama tace"ke tun ɗazu ina jiranki na tsefe kai harsai yayi tsami"murmushi tayi cikin sanyin halinta tace"mantawa nayi sai yanzu ma ni na tuna,ina kibiyar?""a'a ki faɗi gaskiya,Mama tanacan tana yiwa waccan ƴar rigimar tsifar kai shiyasa ta manta da ke"harararsa tayi ta tashi ta koma kusa da Mama ta karɓi kibiyar da Mama take miƙo mata ta fara tsaga kan,"kai ni fa banason wannan shisshigin naka na kwana biyu in kanso ka fito kayi magana kan arigaka dan naga jikar tawa akwai farin jini"Mama ta fada tana yar dariya,shima dariyar yayi ganin Khadee da take shigowa yanzu yasa ya ɗan ɗaga murya wajen faɗin"ai kuwa dai jikarki akwai farin jini dan na lura in nayi sake sai ayi mun kwace,amma ba matsala in an kwace mun ita sai na daure na cije ni kuma na taimakawa karamar tunda ita bata da ko mashinshini"ya ƙarasa da dariyar ƙeta dan yasan ya gama kaita bango,
falon ta shigo tana cin magani tayi wajen Umma ta faɗa cinyarta ta rungumeta sai dai ba kuka take ba ta dai gama shaƙa ne,
cikin lallashi umma ta fara shafa bayanta kafun ta kalli Hammad tace"kama gyara zancenka wannan yarinyar tun tana jaririya ake kamunta kaima kawai ka bada kai dan na fuskanci in da ka dosa",
"Tab Umma dan Allah ku daina haɗa ni da wannan mai bakin jinin ina laifin ma Ameenatuhn"ya fada yana kauda kai"Ameenatuh kuwa tafi karfinka shekara nawa ka bata gaba daya fa baifi shekara biyu zuwa uku ba"haka dai sukayi ta hirarsu anata shakawa Khadee Umma dai tana lallashin abarta.,
Baba ne zaune shida wasu mutane suna hira cikin girmama juna,
"Malam Ishaq yanzu dai tunda Allah yasa abun yazo da sauƙi kuma da sanayya a ciki muna ƙara godiya ga Allah dalilin hakan sannan mujin daɗin bawa Abdallah damar zuwa zance da kukayi,sai dai wani hanzari ba gudu ba in dai yarinya ta amince da yaro gaskiya bamu buƙatar a dau lokaci ba'ayi abun nan ba"murmushi Baba yayi cikin dattako yace"to dama mai ne na daukan lokaci ai kawai da ta amince da shi ni ma a shirye nake dan ni dama banaso ace ta kara wata biyu ba tare da munkaita gidan mijinta ba"haka dai sukayi sallama cike da mutuntawa dangin Abdallah suka tafi,
Shi kuma Baba ya sallami dangi Abban su Ameenatuh domin tunda labarin zuwan baƙi ya iskeshi shima ya bazama neman iyayen Kamalu kuma yayi nassarar samunsu ba tare da wata shan wahala ba ya basu matsayinsu na dangin Uban yarinya.....
*Autar Baba ce*
managarciya