WATA UNGUWA:Fita Ta 34

WATA UNGUWA:Fita Ta 34

WATA UNGUWA:Fita Ta 34

BABI NA TALATIN DA HUƊU

 

 

Ya yi musu gargadin cewa su kula station ba gidan biki ba ne.

Ba don maman Fa'ee ta so ba, a haka ta bar wajen Fa'ee na kuka tare da faɗar "Yanzu Mama a nan zaki bar ni na kwana?"

Yayin da take ficewa daga wurin take faɗar "Ki yi haƙuri ba a son raina zan tafi na barki ba, sai don hakan ya zama dole. Washegari zan dawo, zan san duk yadda na yi na fitar da ke daga wannan wurin."

Akan idon Fa'ee mamanta ta fice daga station ɗin, ta barta a nan tana kuka. A ranta ta ce 'Lallai Sakina ta tabbatar mini cewa ita jinin Iya mai bakin Aku ce.'

 

Bayan komawar maman Fa'ee gidan, gari ya riga ya yi duhu, haka ta isa Ƙofar ɗakinta tare da ciro makullinta daga ƙugunta, da lalabe ta samu da ƙyar ta buɗe ƙofar ɗakin ta shiga.

 

Kasancewar koda ta dawo babu wutàr lantarki, hakan bai dame ta ba, koda yake ba iya ita kaɗai ba kusan dukkan mazauna gidan hakan ba ya damunsu tunda da ma can basu wani saba da wutar lantarkin ba, bare su san dadinta.

 

Hakan ya sa ta shiga lalaben torch light ɗinta, bata wani sha wahala ba ta gano ta, tunda ta riga ta laƙanci wurin da take ajiyewar. Sai dai me ko da ta kunna ta batura sun yi san yi, hasken dishi-dishi yake fita. Dalili kenan da ya saka ta shiga bubbuga jikin fitilar wai ko ta ƙaro ƙarfin haskenta. Tana tsaka da haka kamar daga sama Muryar Julde ta ratsa masarrafar jinta inda take faɗar

"Da ma can wanda yashe zai yi ado da rigar rahin mutunshi garhensa ba ya zama me kyau."

Ɗan jim ta yi kamar bata gane cewa da ita Julde ki yin zancen ba, har sai da Julde ta leƙo kai a cikin ɗakin ta ce "Shannu maman Fa'ee, ki yi ƙoƙarin zawa ɗiyarki kunne, rashin mutunshi ba abun yi ba ne, ɗazu ta sha Ni kuka, yanzu kuma nasan tana shan tana yin shi." Daga haka Julde ta ciro kanta daga Ƙofar ɗakin ta juya.

Maman Fa'ee bata tamkata ba duk da akwai zantuka da yawa a laɓɓanta, amma ta haɗiye su har zuwa lokacin da tura za ta kai ta bango.

 

Wucewar Julde ke da wuya Atika da mijinta suka dawo. Nan fa rikici ya sake ke cewa a gidan, domin maman Fa'ee ba za ta juri ƙananan maganganun da maƙwaftan nata ke yaɓa mata ba. Kaf gidan Iyan Hajje da matar Garba kanuri ne kaɗai basu saka baki a zancen ba.

 

Abinka da gidan haya, kowa ba zai rasa yar guntuwar guzuri-tsomar da zai yi ba.

Ba zancen da yafi ɓata wa maman Fa'ee rai kamar zance Maman shamsiyya da take cewa "Oh! Allah Ya raba mu da bak'ar haihuwa, haihuwar wayyo-wayyo, yarinya kin zama alaƙaƙai a cikin al'umma? Gaskiya da da alama su o'o an yi wankan dauri a banza." Sai ta bushe da dariya.

Sosai wannan zancen ya baƙantawa maman Fa'ee rai har ya sa ta ji cewa sai fa ta mayar da martani sai dai a mutu har liman. Hakan ya saka ta fito tsakar gidan tana faɗar.

"Kananun maganganun nan sun ishe ni, duk wacce take da abin faɗa ta fuskance ni gaba da gaba ba wai ta dinga noƙewa ba. Ke kuma maman Shamsiyya me ma kika ce?"

Ta karkata akalar zancenta akan maman Shamsiyya tana dubanta. Sai dai maman Shamsiyyar tsit ta yi kamar ruwa ya cinye ta.

Ƙwafa ta yi ta ɗora da faɗar "Da dukkan alama waɗanda suka yi dauri a banza suna da yawa a gidan nan. Ba ma gara ni yar daba na haifo ba? Wata kuwa fa? Karuwa ta haifo. Wai har kuti ce za ta cewa kaza ƙazama?"

 

Maman Shamsiyya bata sake cewa komai ba, ta sulale daga wurin, da ma masu azanci sunce idan baki yasan me zai faɗa bai san wanda za a maido masa ba, faɗan da yafi ƙarfinka ka mayad da shi wasa.

Ganin maman Shamsiyya ta bar wurin kuma bata gama bulbular da fetur ɗin rigimar da ta ciko cikinta da shi ba, hakan ya saka ta juya ga Julde da take zaune a ƙofar ɗakinta ta ce

"Ke kuma Bafulatanar gangan me kike cewa ne ɗazu?"

Nan ma Julde bata kula ta ba, ta ci gaba da cin abincinta ganin haka ta ɗora da cewa "da dai kin tamkar, sannan ina so ki sani yin ado da rigar rashin mutunci kan shi matsayi ne, sai isasshe yake iya wannan kalar adon ya zauna daram a jikinsa ba tare da barazana ba..."

A haka ta yi ta zazzage wa Julde kwandon masifa. Da Julden ta gaji da ji sai ta miƙe tana faɗar "Tamkawa yabawa, ƙyalewa mugunyar nakasa."

 

Daga haka ta shige ɗakinta ta bar maman Fa'ee nan tsaye tana kumfar baki.

Tana jiyo sanda maman Fa'een ke faɗar "Komai hassadar mai hassada Insha Allah a goben nan yata za ta dawo, da ma ita hassada ga mai rabo taki ce."

Da alama da kafatarin mutanen gidan take wannan zancen.

 

Washe gari maman Fa'ee tun ƙarfe goma ta fice daga gidan Bargaja ta nufi gidan wani kawunta da yake zaune a garin, ta kai masa kukanta. Shi ya rakata har station aka kashe case ɗin Fa'ee aka basu belinta suka yo gida.

 

Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa jama'ar gidan, kowa da kalar tasa rayuwar ga jahilci da ya yi katutu wa mazauna gidan da ƴaƴansu. Ban da sana'o'in su ba abin da suka sani sai gulma. Yaransu kuwa tsiraru ne waɗanda suke boko, bokon ma a makarantar gwamnati.

 

Ɓangaren shiga banɗaki kuwa har yanzu ba su yada ɗabi'ar jahilcinsu ba, don mace biyu zuwa uku zasu iya haɗuwa a banɗaki ɗaya lokaci ɗaya kowa ya yi nasa uzurin. A ɓangaren yan matan gidan ma haka ne. Maganganun rashin ɗa'a a bakin yaran gidan kuwa ba a cewa komai sai dai ayi kurum.

 

Bayan wani dogon lokaci mamallakin gidan na Bargaja ya saka gidan a kasuwa tare da ba wa mazauna gidan notice na sati biyu.

Wannan al'amari ya girgiza fiye da rabin mazauna gidan, hakan ya saka suka shiga alhini da taraddadi.

A cikin satin nan biyu ba wani rikici da ya sake barkewa a gidan, sai jajantawa juna da suke. Tuni wasu suka saka cigiyar neman ɗakunan haya da zasu ratse su ci gaba da gungura rayuwa.

Kasancewar kusan dukka mazauna gidan hayar ba yan gari ba ne, yan cirani ne daga wasu ƙauyukan masu nisa.

Tun a satin farko Atika suka yi shirin barin gidan. Hakan ya saka ta bi ƙofa-ƙofa tana neman yafiyar Abokanan zamanta da ta cusgunawa.

Maman Fa'ee ma da lokacin ɗagawar su ya yi ta sha kuka haka ta nemi gafarar kowa.

Sai da aka zo tafiya kallo ya koma sama don kuwa har sun kai ƙofa Fa'ee ta juyo da gudu ta rungume Shamsiyya suna kuka da alhinin rabuwa.

Cikin sautin Kuka Fa'ee ke cewa "Tabbas sabo turken wawa ne, ban san cewa na shaƙu da ke kuma ina ƙaunarki kamar yar uwata ba sai yanzu da ranar rabuwa ta zo  Ki gafarta mini Shamsiyya. Ki nema mini afuwar sauran ƙawayenmu da kika san na ƙuntatawa a rayuwa."

 

Daga haka ta juya da gudu ta fice daga gidan tana kuka.

 

Haka jama'ar gidan suka dinga watsewa da ɗaɗ-ɗaya, kafin cikar sati biyu kowa ya bar gidan. Daga lokacin ne kuma rayuwar mutanen gidan Bargaja ta zama tarihi abin tunawa a unguwar.

Bayan cikar sati uku aka rusa ginin gidan gaba ɗaya.

 

UMMU INTEESAR CE