WATA UNGUWA: Labari Game Da Wata Hargitsattsiyar Unguwa Mai Cike Da Abubuwan Al'ajabi
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
*AND NOW*
*WATA UNGUWA*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Free page
P2
BABI NA BIYU
A wannan ranar da misalin ƙarfe 11 na safe, wata ƙaramar yarinya da ba za ta wuce shekaru biyar ba a duniya ce na hango a cikin wani layi tana tahowa daga nesa.
Bata sanye da komai face bante fari wanda tsabar dattin da yayi idan ka gan shi sai ka ɗauka kalar ruwan zuma ne. Fuskarta ta yi face-face da busasshen kunu hancinta dame-dame da majina, kallo ɗaya zaka yiwa jikinta ka fahimci cewa jikinta ya jima bai ga ruwa ba.
Tafe take tana yan wasanninta irin na yara har ta zo ƙofar wani gida, turus ta tsaya tana kallon ƙofar gidan. Turawa ta yi ta ji kofar a rufe gam.b
Da ganin haka ta koma gefen kofar ta zauna tana kuka tana faɗin "Mama! Mama!! Mama!!!"
Wata sassanyar iska ce ta ratsa ta shiga cikin jiki da ɓargonta, ta ƙara takure jikinta guri ɗaya alamun sanyin ya ratsa ta sosai.
Can bayan wani lokaci da ta ga ba alamar dawowar mahaifiyarta yanzu sai ta miƙe ta fara tafiya tana kuka tana shiga gida-gida tana neman Maman nata.
Wani gida ta shiga a layinsu ko sallama bata yi ba.
Matar gidan tana duƙe tana wanke-wanke ta ga yarinya tsaye a kanta tana kuka. ɗagowa ta yi tana duban yarinyar "A'ah! Salma! Lafiya ki ke kuka?"
"Mamata!" Ta faɗa cikin kuka
"Me Maman naki ta yi?" Ladidi ta tambaya.
Cikın shessheƙa ta ce "Ita nake nema bata shigo ba?"
"Bata shigo ba, je gidan yaya Hanne ki duba ta."
Yarinyar ta fice tana ci gaba da kukanta.
Ita kuwa ta ci gaba da wanke-wankenta tana faɗar "Biba ikon Allah! Yau kuma gantalin ya tashi a unguwa ko ina ta shiga ta bar wannan kucakar yarinyar?"
Ganin ba mai amsa mata ya saka ta ci gaba da aikinta.
Salma tana fita ta miƙe hanyar da za ta sada ta da layin gidan yaya Hanne(yayar mahaifiyarta) tana shigowa kan layin gidan dai dai nan wani Babur ya danno cikin layin zai fita, bai yi aune ba ya kaɗe ta.
Ihu ta ƙwala wanda ya gigita shi, bai tsaya ganin ko 'yar waye ba kawai ya ƙarawa babur ɗinsa giya ya fece ya na faɗar "Ku ga yarinya zata jaza mun bala'i yasin ba zan tsaya ba."
Kawu Sadi da ya shigo layin yanzu ya hango abun da ke faruwa sai dai kafin ya ƙaraso gun tuni mai laifin ya gudu.
Da hanzari ya ƙaraso inda take ya tada ta zaune don duba ko ta ji rauni.
Tabbas ta ji rauni, bakinta ya fashe da jini ɗaya daga cikin ƙananun hakoranta masu kama da haƙoran ɓera ya fita, kanta ya fashe sakamakon ƙumuwa da kan ya yi da dutse yayin da take faɗuwar.
Kan kace me, jama'ar layin sun cika gun an kewaye ta ana ta jimami. Wani ƙaramin yaro ne na ga ya juya da gudu ya shige wa gida a layin, zuwa jimawa kaɗan sai ga shi ya dawo tare da Biba da yaya Hanne.
"Innalillahi wa innailaihir raji'un! Salma me ya zo dake nan?" Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka ta rarumi 'yar ta zuwa shagon magani mafi kusa.
Sun mata duk taimakon da ya dace sannan ta saba 'yar ta a baya ta nufi gidanta.
A hanya ta haɗu da Abba, yake tambayar abunda ya faru.
A nan ta gaya mata cewa faɗuwa Salmar ta yi.
Kofar gidan ta buɗe da maƙulli sannan ta sa kai a cikin gidan.
Zo ka ga tsakar gidan yanda ya yi kaca-kaca tamkar makwancin Jaka.
Kwanuka ne ga su nan birjik wasu har sun bushe, sai ƙuda ke bin su buuu!
Tana giftawa zata wuce ƙuda suka tashi buuu, sai sautin kukan ƙudaje kake ji.
Wuce wa ta yi zuwa ɗakinta tana faɗar "Don Allah ji yanda ƙudaje suka cika gida kamar inda aka yi kashi, ni waɗannan banzayen ƙudajen da zan samu maganin kisansu da tuni na ƙarar da su mtsw! Ta faɗa tana jan wani uban tsaki.
Shi ma ɗakin baya shaƙuwa ban da zarnin fitsari ba abunda ke tashi a ɗakin.
Wani tsumma ta Shimfiɗa ta ajiye yarinyar sannan ta fita waje tana faɗar "A'ah! Yau dai har yanzu ba wacce ta shigo gidan nan, ga lokaci yana tafiya ban ɗora komai ba har cikina ya fara kiran ciroma."
Can kuma ta miƙe waje tana leƙen ƙofar gida, ɗaurin kirji ne a jikinta kanta ba ko ɗankwali.
Sadik ne ya zo wucewa nan ta sa baki ta kira shi. "Kai Sadik zo nan."
Ƙarasowa ya yi ta dube shi "Idan ka je gida don Allah kace ina kiran Hanee da Sofi, ina nan ina jiransu yanzu."
"Gaskiya ba gida zani ba, bari dai zan biya na kira sun."
Murmushi ta yi har ƙazaman hakoranta suka bayyana "Yawwa ƙaninmu yi sauri ɗan albarka."
Bai bi ta kanta ba ya wuce abinsa.
Da har zata juya ciki ta hango ɓullowar Nazee, ƙara maƙewa ta yi yanda ba zai hangota ba gudun kar ya gudu.
Sai da ya zo daf da ƙofar gidanta ta dawo dai dai inda take ɗazu ta ce "Nazee namu don Allah zo ka ji."
"Me zan ji ne? Yau dai haka zaki ganni ki bar ni Biba..."
"Habah! Nazee Biba ce fa, kai kasan wannan harƙallar yanda take duk cuɗe ni in cuɗe ka ne, zo ka ji don Allah." Ta faɗa tana yashe haƙora.
Ganin bashi da mafita ya taka zuwa soron gidanta ita kuwa ta koma daga ciki "Ga ni miye?"
Ya faɗa yana haɗe fuska wai don kar ta ga damarsa.
Bata damu da hakan ba ta ce "Nazee don Allah ɗari uku zaka ba ni in yi cefane, yau haka Habibu ya fice bai ban komai ba, banda shinkafar dake ajiye."
"Mijin naki ma ya kasa baki ni me zan iya maki to?" Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa.
"Taimako dai zaka yi irin wanda ka saba, in na dafa ma zan ajiye maka yasin."
Ganin dai Biba ba zata taɓa sake masa kurwa ba in dai ba bata ya yi ba, hakan ya saka ya ciro N200 a aljihunsa ya miƙa mata "iya wannan zaki samu a gurina, kuma Allah ya tsare ni da cin ƙazamin abincinki." Ya juya.
Yana jinsa sanda ta ke cewa "Shege na ji dai je ka ba dai ka bada ba."
Komawa ciki ta yi tana faɗar "aha! Ka ga yanzu na samu ƙari sai na yi cefane da wannan, 500 ɗin da Habibu ya bada ta cefane kuma in sa a bankina, gwanda na tara kuɗin ankon nan da wuri, shi mai zurfin ido daga nesa yake fara kuka. Allah ya kawo mun Hanee na san zan samu ƙari a gunta." Murmushi kawai take ita ta ci banza.
Bayan mintuna talatin sai ga Sofi ta shigo gidan.
"Yawwa Sofinmu zo ki ji."
Me zan miki kuma?" Ta tambaya a gadarance.
don Allah kwanukan nan zaki wanke mun, girki zan ɗora yanzu ga shi ba kwano ko ɗaya a gidannan nan duk sun yi datti."
"Tab ai ni ba jakar gidanku ba ce da zan ci wannan uban wanke-wanken ni kaɗai." Ta faɗa tana ƙoƙarin zama kan tsumman tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan.
"Habah Sofi ki yi haƙuri, yasin zan saka abincin da ke, ki ci sai kin ƙoshi don na san ko kin je gida ma ba samu zaki yi ba." A haka ta ci gaba da lallaɓa Sofi har ta shawo kanta ta amince za ta mata.
Nan Sofi ta shiga haɗa kwanukan yayin da ita kuma ta fice zuwa cefane. Bayan wani lokaci sai gata ta shigo gidan tana faɗar "A'ah! Wai ni kam har yanzu Hanifa bata shigo ba? Wai me take yi ne haka?"
Taɓe baki Sofi ta yi ta ce "Tana can tana kitson kan wata mata, baki ga kan ba kamar an ci goriba da wuƙa, shi yasa ni ba ko wanne kai nake kitsawa ba."
Dariya sosai Biba ta yi yayin da take ƙoƙarin haɗa wuta "Gaskiya Sofi baki da kirki."
A taƙaice sai da Sofi ta kwashe kusan awa huɗu a gidan kafin ta tafi gida bayan ta cika cikinta.
Lokacin ne tana shiga gida ta tarar da ruwa a ƙofar banɗaki ba tare da sanin ko na waye ba ta sunkuci bokitin ta yi ciki a ranta tana faɗar "Rikici ba gado ba kowa ya kwana lafiya shi ya so, in na fito koma ruwan waye sai ayi wacce za'a yi."
Shine fa wannan rikicin ya barke dama ita fitina barci take yi kuma Allah ya laanci mai tashe ta.
Da misalin ƙarfe tara na dare Habibu ya nufo gida tun daga bakin titin unguwar wani ya tare shi ya bashi labarin abun da ya faru da 'yarsa.
Hankali a tashe ya nufo gida, kafin ya ƙaraso gida ya ci karo da wasu mutum uku waɗanda suka tarbe shi da labarin sai dai kowa yanda ya ƙaddara masa aukuwar lamarin dabam.
"Assalamu alaikum." Ya shiga gidan da sallamarsa, sai da ya sallama sau uku ba a karɓa mishi ba amma yana jiyo sautin dariyarsu sai ƙyaƙyatawa suke, dariyar Matarsa tafi ta kowa tashi.
Hakan ya sosa masa rai don haka ya faɗa ɗakin ba tare da sallama ba. Tsawa ya yi cak kamar an dasashi a gurin, ya sake baki yana bin falon da kallo kai daganin yanda ya yi kasan ya ga wani abun da ya matuƙar bashi mamaki ne.
Ba komai ya gani ba face Nura(yaron maƙotansu kuma ɗan uwansa) zabgegen saurayi ne don zai kai shekaru ashirin da uku a duniya kwance yake kan kujera shi da Sagira (yarinyar layin) sun yi kai da ƙafafu ma'ana dai kansa na gurin ƙafafunta itama kanta na gun ƙafafunsa suna fuskantar juna , kanta bako ɗankwali.
Sauran 'yan mata biyu suna kwance a ƙasa yayin da Biba ke zaune a tsakiyarsu da ɗaurin ƙirji, sai suɓalewa zanin yake tana kamawa.
Daga can gefe kuwa yarsa Salma ce a yashe kan ledar ɗakin ba ko shimfiɗa ga filasta a goshinta sai barci take abunta, sai dai kallo ɗaya za ka mata ka fuskanci bata jin daɗin barcin domin sai mutsu-mutsu take ta yi zufa sharkaf, duk da cewa akwai fankar chaji a ɗakin kuma aiki take, sai dai iskanta baya isa gunta.
Ko da suka lura da wanzuwarsa a ɗakin sai suka miƙe kowa ta ja hijabinta sumi-sumi suka bar ɗakin.
Nura ne ya zo ficewa sadda kai ƙasa ya yi yana Faɗar "Sannu da zuwa yaya.."
Har yasa kai zai fice daga ɗakin Habibu ya riƙo hannunsa ya na Faɗar "Dakata!"
Kallo ɗaya zaka yiwa fuskar Habibun ka tabbatar cewa ransa ya kai ƙololuwa gun ɓaci, zai iya aikata komai a wannan lokacin.