Rikicin Jihar Rivers: Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da Fubara ya shigar kan ƴan majalisa 27

Rikicin Jihar Rivers: Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da Fubara ya shigar kan ƴan majalisa 27

Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya shigar na neman tsige ƴan majalisar dokokin jihar su 27 da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, kan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. 

A yau Litinin ne kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar bayan da gwamna Fubara ya nemi janye wa sakamakon wasu batutuwa da su ka sha kan daukaka ƙarar.

Kwamitin mutum biyar, karkashin jagorancin Mai shari’a Uwani Abba-Aji ya bayyana cewa an shigar da wasu batutuwa kan daukaka karar saboda haka aka caji gwamnan Naira miliyan 2.

Daily Trust ta rawaito cewa, tun da fari lauyan gwamnan, Yusuf Ali (SAN), ya nemi a janye batun saboda abubuwan da suka faru sun mamaye shi.

Sai dai lauyoyin bangaren Martin Amaewhule na Majalisar Dokokin Jihar Rivers, da ke jagorancin saurqn yan majalisar 26, Wole Olanipekun (SAN), Joseph Daudu (SAN), wadanda ba su yi adawa da bukatar ba, sun bukaci a yi watsi da batun sannan bayar da Naira miliyan biyu.