Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Tsohon Sarkin Maru Ya Shigar Na Neman Diyar Naira Biliyan 5.6 Kan Cire Shi Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Babbar Kotun Jihar Zamfara da ke Gusau ta yi watsi da karar da sarkin Maru da aka sauke daga Karamar Hukumar Maru, Abubakar Ibrahim ya shigar don kalubalantar tsige shi da kuma tsare shi a gidan Gwamnati, Gusau na tsawon watanni 11.  A cikin waɗanda ake kara sun hada  Sufeto Janar na 'yan sanda Najeriya  da wasu mutane biyar a matsayin wadanda ake tuhuma, kuma ya  nemi diyyar N5.6bn saboda abin da ya bayyana a matsayin cire shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Tsohon Sarkin Maru Ya Shigar Na Neman Diyar Naira Biliyan 5.6 Kan Cire Shi Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Tsohon Sarkin Maru Ya Shigar Na Neman Diyar Naira Biliyan 5.6 Kan Cire Shi Ba Bisa Ƙa'ida Ba

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Babbar Kotun Jihar Zamfara da ke Gusau ta yi watsi da karar da sarkin Maru da aka sauke daga Karamar Hukumar Maru, Abubakar Ibrahim ya shigar don kalubalantar tsige shi da kuma tsare shi a gidan Gwamnati, Gusau na tsawon watanni 11.

 A cikin waɗanda ake kara sun hada  Sufeto Janar na 'yan sanda Najeriya  da wasu mutane biyar a matsayin wadanda ake tuhuma, kuma ya  nemi diyyar N5.6bn saboda abin da ya bayyana a matsayin cire shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

 Amma a hukuncin da ya yanke  a yau  Juma’a, Mai Shari’a Bello Shinkafi ya yi watsi da karar Sarkin, yana mai cewa karar bata da tushe balle makama da kuma rashin cancanta.

 Mai shari’a Bello ya ce kamen da jami’an tsaro suka yi wa sarkin da aka sauke, tare da tsare shi a gidan gwamnati bai saba wa tanadin tsarin mulki ba.

 A cewar alkalin, kundin tsarin mulkin kasar “ya ba jami’an tsaro ikon kamawa da tsare duk wanda ya karya doka.”

 Alkalin ya ce tsare Sarkin da aka yi a gidan gwamnati na tsawon watanni 11 don “tsaron lafiyar sa ne.

 “An bayar da belinsa kuma an ajiye shi a gidan gwamnati don gudun kada talakawansa da suka fusata bisa ga  alakarsa da yan fashin daji da kuma masu garkuwa da satar shanu, kada su yi masa wulakan cin da bai daceba.