Shaikh Bello Yabo yana cikin Malamai masu wa'azi a jijar Sakkwato ya shawarci gwamna Aminu Waziri Tambuwal da ya taimaki addini a sauran lokacin da ya rage masa domin waɗanda suka gabace shi a mulki sun yi ƙoƙari sama da shi.
Malamin a wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafar sada zumunta, Managarciya ta jiyo malamin na cewa "muna yi wa Aminu Waziri nasiha ka dawo ka gyara abin da ka yi wa addini ba ya da yawa.
"Bafarawa ya rabawa malamai da limamai motoci. Alu a kwana 100 farkon mulkinsa ya raba mota 2000 a Sakkwato, haka ya cigaba da rabon motocin har ya sauka, amma wannan kamar an shuka dusa", a cewar Malam Bello Yabo.
Ya ce akwai gyara mu yi masu addu'a ɗan lokacin da ya rage masu su gyara, ko yanzu dai sun yi ɓarna.
"ba mu sun ka yi wa ba, kan su, an yi banza da addini da masu addini duk abin da ya shafi addini ba ruwansu da shi. Babu lokacin da addini da masu addini suka galabaita kamar wannan zamani".
Bello Yabo ya yabawa tsoffin gwamnonin Sakkwato guda biyu waton Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan taimakon addini da suka yi a lokacin mulkinsu.
"Bafarawa ya gina Masallatai da islamiyoyi sama da 2000. Alu ɗan sababi ne tun da ya hau gwamna har yanzu da ya sauka yana gina masallatai ban san yawansu ba, wannan na yanzu nawa suka gina ko ni da nake tare da su ban sani ba", in ji shi.