Saboda Tsananin Kyan Matarsa Magidanci Ya Nemi Alkali Ya Raba Aurensu

Saboda Tsananin Kyan Matarsa Magidanci Ya Nemi Alkali Ya Raba Aurensu

 

Wani magidanci ya shaida wa Kotu cewa ba ya buƙatar tarayya da matarsa, Hilda Mleya, yar kimanin shekara 30 a duniya saboda ta cika kyau. Tribune ta tattaro cewa mutumin mai suna, Arnold Masuka, ɗan shekara 40 a duniya, ya yi wannan ikirarin ne a gaban Kotun yanki da ke garin Lusaka na kasar Zinbabwe. 

A cewar Mista Anold, yana roƙon Kotu ta datse igiyoyin auransa da matarsa saboda tsananin kyaun da Allah ya bata, wanda ke hana shi sukuni da rashin bacci. 
Ya ce yanayin ya yi muni har ta kai ga yana fargabar tafiya wurin aiki ya barta ita kaɗai a gida saboda tsoron wani daban ka iya zuwa ya kwace masa ita. 
Arnold ya ɗauki matakin garzayawa Kotu ta raba aurensa ne saboda ya gano cewa matarsa ta fi kowace mace kyau a lungu da saƙon garin Gikwe na ƙasar Zimbabwe. 
Bugu da ƙari, a bayanan da ya gabatar wa Kotu, ya ce matarsa tana da yawan murmushi a kowane lokaci kuma idan ta yi yana kara mata kyau. 
Amma a cewarsa, abinda yake tsoro da ɗar-ɗar a cikin zuciyarsa, irin wannan murmushin da baya rabuwa da fuskarta ka iya jan hankalin wasu maza, su zo su raba shi da ita. 
Alkalin Kotun, mai shari'a Chenjerai Chireya, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yake jagorantar shari'a makamanciyar wannan.
Da yake yanke hukuncin kan batun, Mista Chireya, ya buƙaci iyayen miji da matar su sa baki, su sulhunta ma'auratan domin samun nutsuwa da zaman lafiya a tsakaninsu.