Abin Takaici Ne Yunkurin Tsige Buhari----Shugaban APC Na Kasa

Abin Takaici Ne Yunkurin Tsige Buhari----Shugaban APC Na Kasa
 

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yunkurin tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da wasu 'yan majalisa suke kokarin  yi lamari ne  abin takaici. 

Adamu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar talabijin ta Trust TV ranar Talata, 9 ga watan Agusta, 2022 a birnin tarayya Abuja. 
Idan baku mance ba Managarciya ta kawo muku rahoton cewa 'yan majalisun tarayya sun yi barazanar fara bin matakan tsige shugaban ƙasa daga kujerarsa a wani taron manema labarai jim kaɗan kafin tafiyar su hutun watanni biyu. 
Mambobin majalisar sun yanke wannan hukuncin ne bayan sun baiwa shugaban ƙasan wa'adin makonni Shida ya shawo kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Da yake maida martani kan batun, shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Adamu ya ce yunkurin babban abun takaici ne, "wanda ya bar kan turba mai kyau.' 
"Shirin shige shugaban ƙasa babban abun takaici ne da babu shi kwata-kwata yanzu. Tare da majalisar tarayya, muna tsammanin irin haka, yana faruwa a ko ina a kowace demokaraɗiyya." 
"A duk lokacin da ya zo kanka, ka cigaba da kokari, hatta waɗan da suka kirkiri yunkurin sun sauya daga kan hanyar."  a cewarsa