Sirrin da ke cikin haduwar Kwankwaso da Ganduje

Sirrin da ke cikin haduwar Kwankwaso da Ganduje
1 / 1

1. Sirrin da ke cikin haduwar Kwankwaso da Ganduje

Sirrin da ke cikin haduwar Kwankwaso da Ganduje

 
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun hadu a filn jirgin saman Abuja kuma suka shiga jirgi daya zuwa Kano abin da ya zo da bazata ga dukkan magoya bayansu a yau Alhamis.
Sanata Kwankwaso wanda yake tsohon gwamna ne a Kano kuma ubangidan siyasar Ganduje sun fi shekara biyar ba su hadu ba a bainar jama'a tun bayan da sabani ya lakume dangantakarsu.
Wannan haduwar ta bazata za ta fito da wasu bayanai tare da bude sabon babin siyasar Kano ganin yanda suka shiga jirgi daya kuma a wurin fitowa Ganduje ya girmama Kwankwaso ya aminta da ya fara fitowa kafin shi da yake Gwamna mai ci a jihar da yake mulki.
Managarciya ta yi hasashen haduwar a wurin Gwamna Ganduje dagangan ne ya aminta da haduwar ganin zai samu labarin Sanata na  wurin, kuma matukar bai bukatar haduwar zai kauce amma ya shigo dakin da Sanata yake zaune ya tafi suka gaisa, irin wadda suka dade ba su yi ba saboda ba su ko ga maciji.
Haduwar za ta zafafa siyasar jihar Kano kuma za ta fito da wasu bayanai na siyasa da mulki a bangaren gwamnati ta kuma bangaren siyasa, duk wanda ya kalli faifan bidiyon fitowarsu a jirgi zai tabbatar da guguwar siyasa ta kada a Kano domin bangarorin biyu sun bude kirjin gabzawa da junansu.