Gwamna Matawalle ya nada sabon shugaban ma’aikata
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya aminta da nada Alhaji Kabiru Muhammad Gayari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jihar.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar bayani, mai dauke da sa hannun darakta janar na fannin harkokin ‘yan jarida, Alhaji Yusuf Idris Gusau, wanda ya rabawa manema labarai a garin Gusau fadar gwamnatin jihar ta Zamfara.
Wannan nadin da aka yiwa Gayari, ya biyo bayan karin girman da tsohon shugaban ma’aikata Alhaji Kabiru Balarabe ya samu na zama sakataren gwamnatin jiha.
Kamar yanda takardar bayanin ta nuna wannan aikin da aka ba Alhaji Kabiru Muhammad Gayari na shugaban tar ma’aikatan jihar Zamfara ya fara aiki nan take.
Alhaji Kabiru Muhammed Gayari, kafin ya samu wannan kujerar, shi ne babban sakataren a ma’aikatar kudi ta jihar Zamfara, kuma shi ne mutun wanda ya dade yana aiki ma’aikatar tsare-tsare da kasafi watau (Budget) tun lokacin da aka kirkiro jihar zamfara, hakama sabon shugaban ya yi zama a matsayin shugaban ma’aikatan ma’aikatar tattara kudaden shiga na cikin gida.





