PDP Shiyyar Kudu Maso Yamma Sun Jijjina Tare Da Tabbatar Da Goyon Bayan Su Ga Ayu

PDP Shiyyar Kudu Maso Yamma Sun Jijjina Tare Da Tabbatar Da Goyon Bayan Su Ga Ayu

 

Masu ruwa da tsaki da sauran muhimman yan siyasa daga bangaren shiyyar Kudu maso Yamma sun jijjina tare da bayyana cikakken hadin kai da goyon baya ga shugaban jam'iyyar PDP na kasa Dakta Iyorchia Ayu.

 
Baya ga jinjinawa da goyon bayansu ga shugaban PDP Ayu sun yaba masa bisa kokarinsa na tabbatar da kasa daya al'umma daya, tare da tabbatar da Dimokuradiyya da kare dokokin Najeriya bisa ka'ida..
 
Fitattun shugabannin PDP, da suka yi taro a Akure, sun jinjinawa Ayu ne bisa kokarin da ya yi na yi wa jam'iyyar ingantaccen jagoranci.
 
Sun kuma yi masa jinjina da irin yadda ya dawo da martabar jam'iyyar, da kara karfafa tsarin Dimokuradiyya abin da yasa jama'a suke rungumar jam'iyyar PDP a duk fadin kasa baki daya.
 
" A halin yanzu PDP na jin dadin irin cikakken hadin kai da aikin tare da juna", inji su.
 
A matsayinsu na shugabannin yankin Kudu maso Yamma, a taron da suka gudanar hakika shugaban PDP Ayu, ya cancanci yabo bisa kokarinsa na ciyar da jam'iyyar gaba, don haka batun da wasu mutane suke yi a kan shugaban ya sauka ba abin saurare ba ne.
 
A cikin wata takardar da suka fitar bayan gudanar da taron mai taken, "Yankin Kudu maso Yamma sun yi magana", shugabanin sun jinjinawa Ayu da ya kawo wadansu abubuwa da dama da ake saran za su taimaka wajen samun nasarar zaben 2023 mai zuwa.
 
 Takardar da suka fitar na dauke da sa hannun shugaban masu ruwa da tsaki yankin Kudu maso Yamma domin hadin kai (SWUF), Cif Ajani Bankole ta kara tabbatar da goyon bayansu ga PDP da shugabanta.
 
Takardar ta kara karfafa wa tare da yin yabo na musamman ga Ayu, bisa kokarinsa na musamman domin ciyar da jam'iyyar gaba ta hanyar yin sasanci da kuma kara karfafa gwiwa, nuna soyayya da tsare tsaren aiki a gabanin zaben shekarar 2023.
 
Shugabanin sun jinjinawa Ayu game da gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar PDP a zaben jihar Osun.