Kotu Ta Bayar Da Umarnin Ƙwace Kadarorin Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Ƙwace Kadarorin Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari
 
 
Kotu ta bada umarnin ƙwace kadarori 10 a Abuja da Kaduna da kuma wasu kuɗaɗe a Amurka ma su alaƙa da tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari.
 
Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin kwacewar wuccin-gadi  na wasu kadarori 10 da  kudade a bankuna, da ake zargin na tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya mallake su ba bisa ka'ida ba.
 
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Mai shari’a Obiora Egwuatu ya ba da wannan umarni ne a ranar Laraba ya yin da ya ke yanke hukunci kan karar da lauyan ICPC, Osuobeni Ekoi-Akponimisingha ya gabatar a gaban kotu.
 
Egwuatu ya ce umurnin na wucin gadi da aka bayar zai dauki tsawon kwanaki 60 don baiwa hukumar ICPC damar kammala bincikenta, daga nan ne hukumar za ta iya neman a kwace kadarorin na dindindin in hujjoji gamsassun sun bayyana.
 
Alkalin ya umurci ICPC da ta bayyana wannan umarni ga duk wani mutum ko masu sha’awar kadarorin na da kwanaki 14 don a nuna cewa kotu ta na da ikon ƙwace kadarorin na dindindin.
 
A cewar ICPC, wasu da ga cikin kadarorin na Maryland da ke Amurka, Abuja, Kaduna da sauran wurare.