Gwamnan Zamfara Ya Rantsar Da Sabon Mataimakinsa

Gwamnan Zamfara Ya Rantsar Da Sabon Mataimakinsa

Sa’o’i kadan da majalisar jihar Zamfara ta tsige Mahdi Aliyu Gusau, daga mukamin mataimakin gwamnan jihar, bayan an sha turka-turka ta siyasa, Gwamna Matawalle ya zabi Hassan Muhammad Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara.

Gwamna ya aike da sunan Sanata Nasiha zuwa ga majalisar dokokin jihar ne, don neman amincewarta, inda kakakin majalisar Nasiru Muazu Magarya ya karantawa zauren majalisar wasikar da gwamnan ya aiko mata.

Nasiha tsohon Sanata ne, wanda Sanata Kabir Marafa ya kayarda shi a zaben 2011, ya sake lashe zabe a shekarar 2019 a inuwar jam’iyyar APC, amma kotun koli ya soke dukkan mukaman da aka zabi jam’iyyar inda ‘yan takarar PDP suka maye gurbinsu.

Bayan awa biyar da Majalisar dokokin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar,Hon Mua'azu Magarya, ta tantance shi, Babbar Jojin Jihar Zamfara,Hajiya  Kulu Aliyu Anka ta rantsar da sabon Mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha