Matsalar Almajiranci a Wannan Zamani Da Hanyoyin Magance Ta

Matsalar Almajiranci a Wannan Zamani Da Hanyoyin Magance Ta

Almajiranci wani tsari ne na neman ilimin addinin Musulunci a kasar Hausa. kalmar ‘Almajiri’ kalma ce ta Larabci, wadda ta samo asali daga kalmar ‘Al-muhajir.’ Ma’ana wanda ya yi hijira daga wani wuri zuwa neman ilimi ko hasken addinin Musulunci.

Almajiranci ya samo asali ne a sanadiyyar girma da fadadar Musulunci, ta yadda ya shiga a cikin lungu da sako na duniya. Sakamakon haka ne mutane suka al’adanci daukar ‘ya’yansu daga garuruwansu zuwa wasu garuruwa a gaban malamai, domin su nemi ilimin addinin Musulunci.

Yaron da aka tura nemn ilimi ta wannan tsarin ana kiransa ‘Almajiri’. A zamanin da ilimin addinin Musulunci ya yi qaranci a mafi yawan garuruwa da qauyuka, wannan ya sa idan mahaifi na son yaronsa ya samu ilimi, to akwai buqatar kai shi wani garin na daban, inda yake da tabbacin akwai malami wanda aikinsa shi ne karantar da xalibbai ilimin addinin Musulunci, domin ya zauna a wurinsa lokaci mai tsawo yana neman ilimi. Zamani na juyawa al’amura na sauyawa ilimin addinin Musulunci na qaruwa yana faxaxa, har ya kai a kusan kowane gari ko qauye yana da yuwa a rasa samun malamin addinin Musulunci, wanda zai karantar da yara. To mine ne ya sanya wannan matsalar ta xauko yara daga wasu garuruwa zuwa birane da sunan almajiranci take cigaba da havaka duk da yawaitar ilimin addinin Musulunci a birane da karkara?

Abin lura a nan shi ne yadda ilimin addinin Musulunci ya yawaita, ya kuma faxaxa a lungu da saqo na birane da karkara, ya kamata kawo yanzu iyaye sun daina xaukar ‘ya’yansu daga garuruwansu zuwa birane da sunan almajiranci. Ya kamata iyaye su canza wannan tunanin, su rinqa barin ‘ya’yansu a garuruwansu su nemi ilimi, da yake ilimin addinin Musulunci ya wadata a kowane gari a Arewacin Najeriya.

Tafiya ta yi nisa an samu canjin yanayi har mutane sun fara kallon almajirai a wannan zamani a matsayin wulaqantacci, waxanda ba su da gata. Yasasshi waxanda iyayensu suka watsar. Wannan xabi’ar ta samu ne saboda canjin lokaci, savanin yadda aka san neman ilimi. Domin a da ko’ina mutum yake neman ilimi, za a gan shi yana zuwa neman ilimi wurin malamai a natse cikin mutunci, ba tare da barace-barace ba. A halin yanzu kuwa, almajiranci ya canza tsari ya xauki wani sabon salo, wanda ke nufin tura yara daga garuruwansu zuwa birane domin samun ilimin addinin Musulunci da kuma neman abinda za a sanyawa a bakin salati. Wannan ya haifar da barace-barace a gidaje, wuraren sayar da abinci da tashishin mota da kasuwanni. Sauyin zamani a yanzu ya sa almajirai sun sauya daga yanda aka san su a da ko dauri. A halin yanzu ba su faye mayar da hankalinsu akan karatunsu ba, sai dai sukan shagala ne da wasu xabi’u marasa kyau waxanda suka haxa da, kallace-kallcen qwallo, qoqarin mallakar wayar hannu, da kallon fina-finai na batsa da na waqoqi da aikace-aikace a gidajen sayar da abinci, tashoshin mota, kasuwanni, filayen qwallo, galibi a waxannan wurare ne sukan ci karo da wasu miyagun xabi’u. Canjin halayya ta almajirai a wannan zamani shi ne ya sa mafi yawancin mutane suke sukar almajiranci. Dalili shi ne da yawansu ana samun su da shiga cikin aikata muyagun laifukan da suka jivanci ta’addanci kamar sata, qwace da satar mutane (don yin garkuwa da su), satar shanu, tayar da hankulan mutane a cikin unguwanni (area boysim). Da yawa daga cikinsu ana kama su da laifin lalata musamman da qananan yara, wannan ya faru ne a sanadiyyar ga-aiki a gidajen sayar da abinci wanda galibin ma su gidajen mata ne ma su zaman kansu.

Iyaye suna sakaci da rashin xaukar nauyin da Allah ya xora musu na kula da karatu da tarbiyyar ‘ya’yansu. Wasu iyayen kan xauko ‘ya’yansu daga garuruwansu zuwa birane, ba tare da qwaqqwaran tanadin isasshen abinci da sutura da sauran abubuwan buqata ba. Da yawan iyayen kan turo ‘ya’yansu ne a lokacin rani, bayan sun kammala girbin abinci a  lokacin damina, a haka za su turo su ba tare da wani guzuri na abinda za su ci ba. Wannan kan sa su yawon garaken mutane dare da rana neman abinda suka ci. Alhali addinin Musulunci bai aminta da bara ba, kuma wannan al’amari na yawan barace-barace ya jefa Arewacin Najeriya cikin qyma da gori,ga sauran qabilu musamman a Kudancin Najeriya.

A gefe guda, malaman da ke karantar da almajirai suna taka rawa a tavarvarewar sha’anin almajiraci. Mafi yawancinsu ba su da wani tsari mai kyau na koyarwa. Sukan karvi almajirai ne ba tare da la’akari da adadin da suke iya kulawa da su ba, babu isasshen wurin kwanansu, babu isasshen ban-xaki (makewayi), babu muhalli tsaftatacce. Bugu da qari, ga yawan cunkoso, wannan babbar barazana ce ga sha’anin kiyon lafiya. Domin a sakamakon haka ake iya samun varkewar wasu baqin cutukan masu saurin yaxuwa zuwa ga al’umma.

Ya kamata gwamnatoci a kowane mataki su xauki wannan tsarin almajiranci da qima, su yi tanadi qwaqqwara idan kashe shi gabaxaya ba zai yiwu ba. Kamar yadda wasu gwamnatoci suke yunqurin kawo gyara ga tsarin da shiri na gwamaya shi da ilimin boko. Ya kamata a yi da gaske gwamnatoci su sanya tsarin almajiranci cikin kasafin kuxi don ganin an gina makarantun allo na zamani kuma isasshi inda za a rinqa karantar da ilimin addinin Musulunci haxi da ilimin zamani tare da ciyar da su, yanda iyaye ba sai sun kawo ‘ya’yansu birane almajiranci ba. A vangaren malaman, gwamnatoci su yi tsari na musamman na kula da inganta rayuwarsu, ta hanyar yanka musu albashi domin su iya xaukar nauyin kansu da ‘ya’yansu. Wannan zai sa gwamnati ta yi doka mai qarfi wadda za ta hana iyaye kawo ‘ya’yansu cikin birane da sunan almajiranci, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga duk malami ko uba wanda ya bijirewa wannan dokar.

 

Abubakar Tukur Muhammad

07060581139/abubakartukur3@gmail.com.