Mata a mukaman siyasa da aikin Gwamnati a Sakkwato

Mata a mukaman siyasa da aikin Gwamnati a Sakkwato

MATA DA MUKAMAN SIYASA DA AIKIN GWAMNATI A CIKIN JIHAR SAKKWATO

    Tun da aka dawo mulkin demokradiyya a wannan kasar a shekarar 1999, gwamnatoci daban-daban sun yi yunkurin tabbatar da mata sun shigo an dama da su a muqaman gwamnati ta hanyar naxa su wasu muhimman muqamai da suka yi daidai da irin gudunmawar da suka bayar a lokutan yaqin neman zabe ko makamancin haka.

    Kamar yadda Gwamnan Jihar ya ambata a wajen taron ranar mata ta duniya ta shekarar 2017, ta bakin Sakataren Gwamnatin jiha Prof. Bashir Garba, in da ya ba da tabbacin gwamnatin Lauya Aminu Tambuwal na baiwa mata tabbacin za ta qara wasu naxexen mata a cikin ta. Qasa da shekara xaya an samu qarin wasu naxe-naden a cikin gwamnati wanda ya nuna gwamnati ta cika wannan alqari da ta xauka.

     Gwamnatin da ke ci yanzu ta Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ta faxaxa hannunta wajen xauko mata da dama domin na da su muqaman siyasa, haka kuma ta yi la’akari da matan da suka chanchanta a cikin aikin gwamnati domin naxa su a matsayin manyan daraktoci da shugabanin hukumomi daban-daban a cikin wannan jihar.

    Duk da yake a baya mata na samun muqamai a cikin gwamnati, amma idan muka yi la’akari da wannan gwamnati za mu tabbatar da an samu qaruwar mukamai sosai da mata ke rike da su.

   Alal misali daga 1999-2015 duka gwamnatocin da suka gabata na baiwa mata muqamin Kwamishinan Harkokin Mata ne kawai a majalisar zartarwa ta jiha. Sai dai an samu qaruwar haka a wannan lokaci in da gwamnatin Mutawalle ta qara kujerun kwamishinoni daga xaya zuwa biyu watau a ma’aikatar harkokin mata inda Hajiya Kulu Sifawa ke riqe da wannan muqami da ma’aikatar ilmin sakandare da firamare a wannan jihar in da aka naxa Prof. Aisha Madawaki a wannan muqamin.

     Idan muka duba a muqaman masu baiwa gwamna shawara an samu kaso mai yawa na matan da aka naxa a waxannan muqaman, inda suke rike da jerin masu baiwa gwamna shawara kamar haka;

  1. Hukumar ilmin manya ta jiha
  2. Hukumar ilmin ‘ya’ya mata ta jiha
  3. Hukumar Kula da ilmin manya ta Jiha
  4. Hukumar Kula da Qananan da Matsakaitan Masana’antu ta jiha.

   Haka kuma a fannin aikin gwamnati wannan gwamnati ta yi  hubbasawa wajen ganin an naxa mata a muqaman manyan Daraktoci da Manyan Sakatarori.

    A halin yanzu mu da babbar sakatariya a ma’aikatar Harkokin Mata ta jiha, watau Lauya Aishatu Muhammad Dantsoho da manyan daraktoci da suka hada da babbar Darakta a Hukumar Qanana da Matsakaitan Masana’antu ta wannan jiha, Hajiya Aisha Turai, da hukumar Ilmin ‘ya’yan mata, Hajiya Halima S/Tudu da Babbar Daraktar Kula da Gadinoni da wuraren shaqatawa, Hajiya Amina Jekada. Sauran sun haxa da Babbar Daraktar Kula da Hukumar kula da  Dorewar Muradun Cigaba, watau (Sustainable Development Goals MDGs)

    Akwai mata da suke riqe da muqamin Masu Baiwa Gwamna Shawara har guda hudu da suka haxa da mai baiwa Gwamna shawara kan qungiyoyin jinqai da ba na gwamnati ba watau (NGO) Dr. Hafsat Galadima, da ta Hukumar Ilmin Mata ta jiha, watau Dr. Amama Yusuf da ta Hukumar Ilmin Manya, Hajiya Binta Muhammad Gwadabawa da kuma  mai baiwa gwamna shawara a hukumar ilmin mata  Hajiya Aisha Musa Maina.

     Yunqurin da mata ke ta yi na neman kashi talatin da biyar 35% a cikin muqaman gwamnati a dukkanin matakai zai xau lokaci kamin cin ma wannan, sai dai sannu-sannu a na samun qari, kamar yadda ma su iya magana ke cewa “ Da yayyafi kogi ke cika”

   Duk wannan a vangaren zartarwa ne, amma abin da ya shafi sashen Majalisar Dokoki ta Jiha, tun da aka dawo mulkin farar hula yau shekaru goma sha tara, an ka sa samun wata kallabi a tsakanin rawunna a wannan majalisa. Abin jira mu gani, ya rage qasa da sheakara xaya al’ummar wannan jiha za su koma a runfunan zave, wata qila a wannan karon zata chanja zane domin an fara samun mata sun qara yunqurowa domin samun wakilci a majalisar dokoki ta jiha.