.....Kar Ku Bari A Haɗa Kai Da Ku Wajen Yaɗa Labarun Ƙarya-----Shugaban 'Yan Jarida

.....Kar Ku Bari A Haɗa Kai Da Ku Wajen Yaɗa Labarun Ƙarya-----Shugaban 'Yan Jarida

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Shugaban 'yan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, (internet) reshen jihar Kano, Hisham Habib, yayi kira ga 'ya'yan kungiyar da kada su bari ayi amfani dasu wajan yada labaran ƙarya marasa tushe ko yada jitajita duba da karatowar zaben shekara mai zuwa (2023).

Shugaban yayi Kiran ne lokacin taron ganawa da juna na musamman da kungiyar ta gabatar ranar Asabar a Kano.

Acikin Jawabin sa da ke dauke da sa hannun Sakataren kungiyar, Yakubu Salisu, Hisham yace Kiran ya zama wajibi duba da yadda  kafafen yada labaran internet ke da tasiri a acikin al'umma, kuma  kowa ke amfani da wayar sa wajan bibiyar me ke faruwa a duniya.

Kazalika ya ce ina kira da babbar murya ga 'ya'yan kungiyar da su kasance kwararru akan aikin su ako da yaushe, sanan ya kuma ya yi  kira ga al'umma da ma'aikatu da su tantance kafafen yadda labaran da za su yi mu'amula da su.