Ranar NTD Ta Duniya:Mutane  Miliyan 4 na fuskantar barazanar cutar Ciwon Dundurmi a Zamfara 

Ranar NTD Ta Duniya:Mutane  Miliyan 4 na fuskantar barazanar cutar Ciwon Dundurmi a Zamfara 
 
 Daga Hussaini Ibrahim.
 
 Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Abubakar, a ranar Talata, ya ce,binciken alkalumma da aka gudanar a jihar ya nuna cewa sama da mutane miliyan hudu ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta Dundurmi a dukkanin Kananan hukumomi shahudo na jihar.
 
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron tunawa Ranar NTDs ta Duniya da ya gudana a dakin Taron karo na uku na Hukumar (NTDs) da aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar Lafiya da ke Gusau,babban birnin Jihar Zamfara.
 
  Kwamishinan ya kara da cewa dukkanin qananan hukumomi shahuxo na fuskantar barazanar da cutar yayin da sama da mutane miliyan 4 da ke zaune a jihar ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta Dundumi.inji Hon Aliyu Abubakar.
 
   Shirin "NTDs na fiye da mutane biliyan 1.7 a duniya ke amfana da Shirin .
 
 Ya ce yawanci wadanda suka kamu da cutar ta NTD (cututtuka) galibi ana nuna musu kyama kuma hakan kadai zai iya yin illa ga wadanda abin ya shafa ko kuma iyalansu.
 
 Ya ce, “Cutar ba ta shafi Lafiyar mutane kadai ba, har ma tana dauke musu damar zuwa makaranta ko kuma samun abin dogaro da kai.
 
 "Maganar da ke tattare da hakan na iya yin mummunar tasiri ga wadanda abin ya shafa da kuma iyalansu da al'ummominsu."
 
 Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar Zamfara qarqashin jagoranci gwamna Matawale na yin abun da ya kamata wajen ganin an kawar da cutar ta NTD a jihar, inda ya jaddada cewa Najeriya baki daya musamman jihar Zamfara na cikin hadarin kamuwa da cutar ta NTD.
 
 Ya kara da cewa "kananan hukumomi 7,ke fama da Cutar Amosanin Ido. kuma Dalibai  yara sama da miliyan 1.1ke fuskantar matsalar Ciwon mafitsara.
 
 Shugaban Shirin na Hukumar Sightsavers ,Ahmad Ibrahim ,ya tabbatar da cewa, Hukumar zata cigaba hada gyuwa da ma'aikatar lafiya ta jihar Zamfara,wajan yaki da waxannan cututuka da suka addabi al'umma.