Za'a Yi Bukin Cin Naman Kare A Jihar Gombe
Za'a Yi Bukin Cin Naman Kare A Jihar Gombe
Kwamitin shirye-shirye na bikin cin Naman kare na al’ummar Tangale dake garin Billiri a jihar Gombe sun shirya farfado da dadaddiyar al’adar su da suka dai na na bikin cin Naman kare “Bikin da aka yiwa take Lo-Bai, ko Palam Tangle da ake cin Naman kare.
Bikin da za’a gudanar na tsawon kwanaki uku ana yi dan cin Naman Kare a kasar Tangale sannan kuma za’a gudanar da lacca wa al’umma a kowacce da za’ayi bikin.
Wannan batu yana dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannayen Jessy Mallums mai Dukkan Tangale shugaban kwamitin gudanar da shirye- shiryen da kuma Sakataren sa Dulyamba Alkeria Bagauda, da suka aikewa manema labarai, inda suka nuna cewa bikin cin Naman karen na Palam Tangle zai gudana ne a garin Billiri a ranakun 26 da 28 na wannan wata na Disamba na 2021
Kamar yadda takardar ta nunar bikin na ranar cin kare yana daga cikin muhimman ranakun wasan gargajiyar Tangale da aka dai na gudanarwa tsawon lokaci bayan an gano gibin da rashin gudanar da wasannin a ya haifar a tsakanin Yaran da suke tasowa sai kwamitin gudanarwa suka hada kai dan ganin an dawo da wannan al’ada.
A cewar su wannan wasa na al’ada yazo dai dai da na yan kabilar Ngas dake jihar Filato da suma suke gudanarwa duk shekara, inda suka ce nasun ma bai da wani banbanci da na Angasawa.
Kwamitin yace wasan al’adan cin kare yana taimakawa sosai wajen bai wa yan kabilar Tangale dama suna alfahari da ciyar da al’adun su gaba, yana kuma kawo hadin kai da bude ido sannan yana bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samar da aikin yi a kasar Tangale.
“ Kamar mu kananan Yara da muke tasowa za mu dauki abun zuwa sama dan karfafa al’adun mu na ganin bamu bari al’adar mu ta mutu ba saboda daddaren tarihi da muke da shi yanzu za mu fara da wannan” in ji su.
Ganin muhimmancin wannan rana a ranar farko za’a gudanar da lacca mai taken “TANGALE MAN AND HIS IDENTITY”, ma’a Batangalen Mutum da shaidar sa, inda a za’a yanka Kare a dafa shi a ci Naman kyauta a wannan waje.
Rana na biyu a gudanar da lacca mai take JUSTICE AS A FOUNDATION FOR PEACEFUL COEXISTENCE- wato adalci ginshikin zaman lafiya mai daurewa, a gefe guda a bada dama a sayar da Naman kare wa sababbi da tsofaffin abokan cinikayya wato kwastomomi.
Sannan a rana na uku ayi lacca mai taken KAL KWI KA AMDO SHUM SHAN TONDOWEI (hadin kai, kaunar juna, da ci gaba) inda nan ma a gefe guda za’a karisa sayar da Naman Karen da aka fara washegari wa masu ruwa da tsaki, sannan har ila yau a nuna wasu kayayyakin gargajiyar Tangale.
Makera, masu kere-kere masu magungunan gargajiya da sauran su kowa zai baje kolin kayan gargajiyar sa da gadon gidan su a lokacin da ake baje kolin kayayyakin.
managarciya